‘Yan Majalisar Wakilai ta Ƙasa su uku daga Jihar Katsina sun fice daga APC, sun koma PDP ƙarƙashin rundunar yaƙin kamfen din Atiku Abubakar.
Su ukun da su ka haɗa da mai wakiltar Katsina, wato Salisu Iro, sai Hamza Dayyabu mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Rimi, Charanci da Batagarawa, sai na uku Ahmed Ɗayyabu mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Ɗanmusa, Batsari da Safana.
Majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa ne ya yi masu iso wurin Atiku, ranar Lahadi da dare a Sokoto.
Majiyar ta ce su ukun su na cikin rundunar Atiku da ta dira kamfen a Zamfara a yau Litinin.
APC a Katsina na shan fama da rikici, wanda ya yi ƙamarin da Sanata Babba Kaita mai wakiltar Shiyyar Buhari, shi ma a cikin 2023 ya fice daga APC, ya koma PDP.
Shi ma Mustapha Inuwa, sun raba gari tsakanin sa da Gwamna Aminu Masari, domin tuni ya koma PDP.
‘Yan Majalisa uku da su ka fice daga APC su ka koma PDP, duk ba su samu damar tikitin tsayawa takara a 2023 ba.
Discussion about this post