Mai Girma Gwamna Cike Da Girmamawa Tare Da Yima Fatan Al’heri Da Fatan Samun Nasara A Dukkanin Al’amurranka.
Mai Girma Gwamna Zanyi Amfani Da Wannan Dama Domin Inyi Kira Zuwa Gareka A Bisa Matsalar Tsaro Da ta Addabi Al’ummar Ƙaramar Hukumar Mulki ta MARU Yankin Dansadau, Babu kamar wannan Gari na Mutunji, masarautar Mutunji kadai tanada kauyuka sama da Talatin (30)
Karkashin ta.
Mai Girma Gwamna Al’ummar wannan yanki na Mutunji Basu Taɓa Samun Kansu A Cikin Matsanincin Hali Ba Na Rashin Tsaro Ba kamar Irin Wannan Lokaci Damuke Ciki Bah.
Mai Girma Gwamna Samar Da Tsaro Da Ilimi Da Hanyoyin More Rayuwa Da Ingantaccin Ruwan Sha Na Ɗaya Daga cikin Hakkin Da Allah S.W.A Ya Rataya Maka Na Al’ummar Jahar Zamfara A Kanka Yana Da Kyau Ace Kayi Wata Hubɓasawa A Kan Waɗannan Al’amurra Domin Sauke Nauyin Da Allah S.W.A Ya Rataya Maka A Kanka.
Ko Shakka Babu Mai Girma Gwamna ka yi kokari Sosai wajan Ganin cewa An kawo Karshen Matsalar Tsaro Afadin Jahar Zamfara Baki d’aya.
Mai Girma Gwamna Muna Ƙara Miƙa Ƙoƙon Baran Mu Zuwa Gareka Da A Duba Yiyuwar Magance Wannan Matsala Ta Rashin Tsaro ta Hanyar Tura Jami’an Tsaro ‘yan Sanda, Da Sojoji Na dindin a wadannan Kauyuka kamar haka:-
1. Mutunji
2. Malele
3. Randa
Mai Girma Gwamna yanzu haka ko Out Force na ‘yan Sanda Babu a wannan yanki ma’ana ko Dan Sanda Guda Babu a wannan yanki na Mutunji.
Mai Girma Gwamna ba daidai ba ace mutane su ne zasu ginda daukar doka a hannun su ba wannan ba daidai ba ne.
Da haka Al’ummar wannan yanki Suke Roƙon Ubangiji Allah S.W.A Ya Baka Damar Tura masu Jami’an Tsaro
Domin Magance Wannan Matsalar ta Tsaro.
Allahuma Amin.
Umar Adamu Mutunji, shi ne uban kasar Mutunji dake a Karamar Hukumar Maru Jihar Zamfara
Discussion about this post