Ɗan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin APC, Bola Tinubu, ya yi alƙawarin magance dukkan matsaloli da ƙalubalen da tsarin almajirci ke fuskanta a Arewa, idan ya zama shugaban ƙasa.
Tinubu ya yi wannan alƙawarin a Kano, a ranar Talata, a lokacin da ya yi taron ganawa a zauren taro da manyan limamai da malaman addinin Musulunci daga jihohi bakwai na Arewa maso Yamma.
Tinubu ya ce gwamnatocin da su ka shuɗe sun kasa warware matsalolin da almajirci ke fuskanta, saboda rashin kyakkyawan tsarin da ba su shata ba.
“Bari na amsa tambaya kan tsarin almajirci. Ta yaya za a magance matsalar almajirci a gwamnatin da ta gina makarantu amma babu ƙananan asibitocin da almajiran za a riƙa kula da su? Ba a tsara albashin malaman su ba, ba a yanka masu alawus-alawus ba.”
Haka Tinubu ya bayyana a lokacin da ya ke sukar tsarin karatun Tsangaya, wanda gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ta ƙirƙiro a Arewacin Najeriya.
Ya yi alwashin bai wa tsarin ilmi muhimmancin da matasa za su amfana sosai fiye da gwamnatocin da su ka gabata.
“Kowane yaro ya na da ‘yancin ya samu ilmi. Ba daidai ba ne matuƙa a bar yara su na ta gararamba a kan titina, su na fama da fatara da talauci da ƙuncin rayuwa.
“Idan aka zaɓe ni, zan kafa hukumar inganta karatun almajirai, kuma hukumar za ta yi aiki da ku malamai da limamai domin a kawo ƙarshen matsalolin da su ka dabaibaye almajirci.”
Majalisar Ɗinkin Duniya dai ta ce akwai yara ƙanana miliyan 20 masu gararamba kan titina ba su zuwa makaranta.
A wurin taron wanda Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ya shirya, Tinubu ya roƙe su cewa su zaɓe shi. Ya ce shugabannin addini musamman malaman musulunci matsayin su ya wuce na masu koyarwa kawai.