Shugaban kasa Muhammadu Buhari da dan takarar shugaban Kasa na APC Bola Tinubu ba su iya gabatar da jawabi ba a taron kamfen na APC da aka yi a jihar Bauchi ranar Litinin.
Jim kadan bayan fara taron, na’urar sautin ta daina aiki kuma duk kokarin da ake yi na ganin an gyara na’urar ya ci tura. Bayan an dade ana jira, Shugaban kasa da Tinubu sun bar wurin ba tare da yiwa magoya bayan jam’iyyar jawabi ba.
PREMIUM TIMES ta lura cewa na’urar sautin ta daina aiki ne a lokacin da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu ke shirin kiran shugaban kasa da dan takarar shugaban kasa su yi magana.gabatar da jawabin su.
Sai dai duk da haka shugaban Buhari ya mika wa dan takarar APC, Bola Tinubu tutar APC.
A jawabin da dan takarar gwamnan jihar na APC yayi ya yi alkawarin Sadique Abubakar, ya ce idan ya zama gwamnan Bauchi zau kawo sauye-sauye na ci gaba da ba ataba samun irin su ba ajihar.
” A yau a asibitocin Bauchi mata 1,549 ne ke mutuwa a cikin kowacce 100,000 da suka haihu. Wannan ya nuna cewa gwamnati ta yi sakaci, za mu magance wannan matsala ta hanyar tabbatar da samun kulawar likitoci a fadin jihar ta hanyar gina karin asibitoci da samar da kayan aiki domin mutanen mu wadanda ba su da lafiya.
” Sannan kuma ina kira ga dukkan tsoffin gwamnonin jihar su zo mu hada hannu da ni mu fatattaki PDP a jihar Bauchi, mu kawo ci gaba mai ma’ana.
Discussion about this post