Babban bankin Najeriya ya lashi takobin kakabawa duk wani bankin da aka samu yana ɓoye sabbin takardun kudi hukunci mai tsauri idan aka same su da haka.
Shugaban babban bankin CBN reshen Kano Umar Biu ne ya bayyana hakan a lokacin wani shirin wayar da kai kan sabbin takardun kudi da aka shirya wa ƴan kasuwa a kasuwar Sabon Gari da ke Kano.
Biu ya hori ƴan kasuwan su kai ƙarar duk wani banki da aka samu yana ɓoye sabbin takardun kudi ko kuma ya ki karbar tsoffin takardun kudin kafin ranar 31 ga watan Janairu 2023.
Babu wani banki da zai ki karbar tsoffin takardun kudi har sai ranar 31 ga Janairu, 2023.
Wannan shiri na wayar da kan jama’a an yi tattaki har zuwa Kasuwar Kwari, Kasuwar Canji ta Wapa, Kasuwar Kofar Wambam da kuma shahararriyar kasuwar Kurmi ta Kano domin a faɗakar da ƴan kasuwa.
Tun a ranar Larabar da ta gabata, Daraktan Sashen Shari’a na CBN, Kofo Salam-Alada, ya bayyana cewa tuni CBN ke sanya ido a kan bankunan da ke ci gaba da raba tsofaffin takardun naira daga na’urorinsu na ATM.
Salam-Alada wanda ya bayyana haka a lokacin wani shirin wayar da kan mutane game da sabbin takardun kudi na Naira a Legas inda ya bukaci bankunan da su gaggauta rika biyan mutane da sabbin takardun kudi cikin gaggawa.
“Zan iya gaya muku a yau cewa CBN yana fitar da sabbin takardun kudi a kullum. Kamar yadda muke magana, bankuna na can CBN suna karbar kudi. A gaskiya muna rokon bankuna da su zo su karbi kudi daga babban bankin kasa. Muna da wadannan sabbin takardun kudi na Naira a rumbun ajiyarmu kuma muna rokon bankuna su zo su kwashe su,” inji shi.
A watan Oktobar shekarar da ta gabata ne Gwamnan Babban Bankin CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana shirin sake fasalin kudin Najeriya N200, N500 da N1,000. Ya ce sabbin takardun za su fara yaduwa a watan Disamba yayin da ake sa ran yan Najeriya za su canja duk tsoffin takardun kafin ranar 31 ga Janairu.
Discussion about this post