Kwamishinan Hadinkan Jama’a da bunkasa kananan masana’antu na jihar Bauchi Sa’adatu Kirfi ta sauka daga mukamin Kwamishina ranar Alhamis.
A wasikar ajiye aiki da ta yi, Kirfi ta mika godiyarta ga gwamnan Jihar Bala Mohammed bisa dama da ya bata na yin aiki a ma’aikatar bunkasa kananan masana’antu na jihar. Ta yi wa gwamnatin fatan Alkhairi.
Bayan haka mai baiwa gwamnan jihar shawara kan harkokin kananan hukumomiHaruna Guyuba, ya ajiye aiki. Shima ya godewa gwamnan bisa damar da ya bashi na dashi mai bada shawara a mulkin sa.
Duka wadannan ajiye aiki na da alaka da tsige Wazirin Bauchi da sarkin Bauchi yayi wanda ke da alaka da sabani da ya shiga tsakanin gwamnan jihar Bala da wazirin Bauchi, Bello Kirfi.
Tsige Bello Kirfi daga sarautar Wazirin Bauchi
Sarkin Bauchi, Mai martaba Rilwan Adamu ya tsige Wazirin Bauchi, Bello Kirfi wanda shine mahaifin Sa’adatu sannan kuma uban gidan Guyuba saboda sabani tsakanin sa da gwamnan jihar Bala Mohammed.
A cikin wasikar da aka aika wa Wazirin Bauchi, Bello Kirfi, wanda PREMIUM TIMES ta gani, sarki Adamu ya ya amince da tsige Waziri Kirfi daga sarautar Wazirin Bauchi, sannan kuma ya cire shi da ga majalisar masarautar Bauchi.
” Saboda adawa da rashin biyayya da kake yi wa gwamna Bala Mohammed, masarautar Bauchi ƙarkashin Mai martana Rilwanu Adamu ta tsige ka daga sarautar Wazirin Bauchi.
” Bayan haka kuma an cire ka daga majalisar masarautar Bauchi.
Bello Kirfi yana da kyakkyawar alaka da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
A kwanakin baya, gwamna Bala ya rubuta wa shugaban jam’iyyar PDP, Ayu wasikar cewa wasu jigajigan PDP a jihar dake da kusanci da ɗan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar da yi wa takarar sa zagon kasa.
Ko da yake bai faɗi ko su wanene ba, majiya ta shaida cewa Bello Kirfi ne ne, da tsohon kakakin majalisar tarayya, Yakubu Dogara da Abdul Ningi.
Bayan haka alakar dake tsakanin su ya dada tabarbarewa.
Idan ba a manta ba , wannan ba shine karon farko da Sarkin Bauchi ke tsige hakiman masarautar sa.
Ya dakatar da Jakadan Bauch, Yakubu Dogara, Ya dakatar da Yakubu Shegu, Wakilin Bauchi sai kuma yanzu da tsige Wazirin Bauchi, Bello Kirfi.