Babbar daraktan kula da ƙungiyoyin jama’a na kwamitin yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC. Naja’atu Mohammed ta yi murabus daga siyasa kwatakwata.
Fitacciyar ƴar siyasar ta muka takardar ta ga shugaban jam’iyyar Adamu Abdullahi ranar 19 ga Janairu.
Naja’atu ta ce ba za ta iya ci gaba da yi wa ɗan siyasar aiki ba, saboda gaba ɗaya jam’iyyu da ƴan siyasa Najeriya basu da bambamcin akida dukkan su jirgi ɗaya ya kwaso su.
Ta ce yadda ake siyasa yanzu a kasar nan ba za ta iya ba, bai dace da irin ra’ayi da manufofinta ba, saboda haka ta janye da ga farfajiyar siyasar Najeriya yanzu.
Na rubuto muku wannan wasika ne domin in sanar da ku cewa na fice daga jam’iyyar APC. Sannan kuma i na sanar da ku murabus ɗina a matsayina na daraktan kula da ƙungiyoyin jama’a na kwamitin yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.
” Abin alfahari ne yin aiki da kai (Malam Adamu) don ba da gudummawarmu don gina al’ummarmu. Sai dai duk da haka, da dama daga cikin abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a fagen siyasa a kasar nan, sun sa ba zan iya ci gaba da a dama dani a harkokin siyasa ba.
Bayan na yi nazari mai zurfi sosai, na yanke shawarar janyewa daga siyasar jam’iyya. Na fahimci cewa tarbiyata da horo ta ba su dace da siyasar jam’iyya ba. Jam’iyyun siyasarmu ba su da bambancin akida kuma kawai riguna ne da ‘yan siyasa ke sanyawa don biyan bukatunsu a kowane lokaci. A dalilin haka ne muke ganin ‘yan siyasa suna canja sheka daga wannan jam’iyya zuwa waccan a duk lokacin da suka ga kawai hakan ya bijiro musu don siyasar su.
Discussion about this post