A hira da PREMIUM TIMES ta yi da wata manomiya mai suna Bukola Fadairo wacce ta karanta darasin kerekere a Jami’ar Minna jihar Neja amma ta tsindima cikin harkokin noma a jihar Oyo, Bukola ta ce ta shiga harkar noma ne saboda rashin aikin yi da ake fama da shi a kasar nan.
Ta ce a yanzu haka tana noman tumatir, Kankana, kwakwan manja, rogo, kankanba, masara da kubewa kuma tana samun kudi sama da Naira 300,000.
Bukola ta ce ta fara noma a shekaran 2018 bayan ta kammala bautar kasa ta nemi aiki kuma bata samu ba.
Ta ce a lokacin ta na da sauran kudaden da ta tara sannan wani dan uwanta ya shawarce ta da ta shiga sana’ar saro garin kwaki tana sai dawa.
“Na fara sana’an kuma a lokacin ina samun kudi sai dai kuma daga baya sai na gaji da shi.
“Daga nan sai dan uwana ya ce na shiga harkan noma da a lokacin na fara da noman kubewa da kankana.
“Na siya wasu filayen sannan wasu Kuma na karbi hayan su inda daga nan ne na fara noman tumatir, kwakwan manja, Kankana, rogo da masara.
Bukola ta ce tana siyar da amfanin gonan da ta noma daidai gwargwado.
“Misali nakan jira ana gobe kasuwa ko kuma ranar kasuwa kafin na cire kubewa daga gonata na siyar a kasuwa saboda kubewa kan lalace da wuri.
Daga nan Bukola ta ce rashin samun ma’aikata na gari da za su rika yi mata aiki a gona na daga cikin manya matsalolin da take fama da su.
“Wasu ma’aikatan kan gudu mun da kudi ba tare da sun yi mun aiki ba wasu kuwa za su karbi kudin sannan ba za su yi aikin yadda ya kamata ba.
Ta ce sauran matsalolin sun hada da rashin samun ruwa musamman ga manoman dake noman rani, amfani da maganin feshi wanda ke rage amfanin noman da ake samu, tsadar takin zamani da barnar da shanu ke yi wa manoma a gonakinsu.
Discussion about this post