Ohinoyi na Ebira Mai martaba Ado Ibrahim ya bayyana dalilan da ya sa bai halarci taron kaddamar da ayyukan a garin Okene ba wanda shugaba Muhammadu Buhari ya halarta.
Ohinoyi Ado ya ce kamar yadda mutan gari suka ji wai shugaban Kasa zai ziyarci garin Okene haka shima ya ji. ” Abin mamaki ma shine wai shugaba Buhari zai kaddamar da fadar sarki wanda ni ban sani ba. Fadar da na sani shine fadar da ni nake ciki tun 1997 da aka nada ni Ohinoyi na Ebira.
” Na samu takarda daga ma’aikatar kananan hukumomi da masarautun jihar Kogi cewa wai gwamna zai kaddamar da wasu ayyuka a garin Okene, ranar jajibarin ziyarar. Tsakani da Allah a matsayina na basarake mai cikakken iko a wannan yanki, a ce wai sai da ya rage awoyi ne za a aiko mini da takardar sanarwa, ba na gayyata ba a garin da nake sarauta.
Sannan kuma ada safiyar wannan rana, sai aka samu hatsari na fashewar Bom a kusa da fada ta. Babu wanda ya damu da abinda ya faru. Ko ni ba zan iya fitowa wurin taron ba saboda jami’an tsaro sun kange wurin kaf, babu shiga ba fita, sannan cikin fadata kuma akwai mutane suna kwance ana kokarin kula da su wadanda suka ji rauni.
Saboda abin a shirye yake aka dauko wani basarake dabam aka bashi wata takarda da sunana wai yana wakiltata a wurin taron. Ni ban san da hakan ba.
Duk korafekorafen da gwamnati ta rubuta akai na lallai ba a yi min adalci ba kuma bai dace da ni ba a matsayina na babban basarake a wannan yanke sannan sananne a ba ma a Najeriya ba har da kasashen duniya.
Idan ba a manta ba gwamnati Kogo karkashin gwamna Yahaya Bello ta aika wa ohinoyi Ado Ibrahim, takardar korafi kan rashin halartar kaddamar da ayuka da gwamnan yayi a garin Okena da ya samu halarcin shugaban Kasa Muhammadu Buhari.