Tsohon gwamnan jihar Adamawa ya bayyana wasu dalilai da suka sa ya hakura da ci gaba da zama a jam’iyyar APC .
A takarar bankwana da yayi wa jam’iyyar wanda ya aika wa shugaban jam’iyyar na mazabar sa a jihar ya ce dalili na farko wanda shine kuma muhimman dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar shine na rashin hadin kai da warware matsaloli da ya cukuikuye jam’iyyar.
Bindow ya ce tare dashi duka magoya bayan sa duk za sun tattara nasu ina su sun fice daga APC.
Bayan haka ya ce tun daga 2019, aka samu baraka a cikin jam’iyyar, hakan ya sa kowa yaka ma gaban sa yana abinda ya ga dama. Jam’iyya ta kasa kiran mu gaba daya a samu hadin kai domin ci gaban jam’iyyar. Haka ake ta zama cikin matsaloli na yau da ban da na gobe.
Discussion about this post