Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa Kasafin 2023 hannu a ranar Talata, wanda a yanzu ya zama doka. Kasafin dai a yanzu ya koma naira tiriliyan 21.8, ba naira tiriliyan 20.5 wanda Buhari ya aika Majalisa ba.
Majalisa ce ta lafta ƙarin naira tiriliyan 1.3 kan kasafin, wanda shi ne kasafin ƙarshe da gwamnatin Buhari ta yi, kafin saukar ta a ranar 29 Ga Mayu 2023.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Majalisar Dattawa ta damƙa wa Buhari kasafin 2023, ta lafta naira tiriliyan 1.3 kan abin da Buhari ya kasafta na naira tiriliyan 20.5 tun farko.
Majalisar Dattawa ta amince da kasafin naira tiriliyan 21.8, wanda hakan na nuni da cewa sun yi ƙarin har naira tiriliyan 1.3 a kan naira tiriliyan 20.5 ɗin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kasafta a cikin watan Oktoba.
A yanzu kasafin zai koma naira 21,827,188,747,391.
Dattawan Majalisa sun ƙara gejin farashin fetur a ma’aunin kasafin kuɗi da kuma ma’aunin kasafin kuɗi bisa mizanin farashin gangar ɗanyen mai a duniya.
Sun maida gejin mizanin awon kasafin kuɗi daga dala 70 zuwa dala 75 a matsayin farashin gangar ɗanyen man fetur ɗaya.
An tsara kasafin Najeriya bisa mizanin yawan gangar ɗanyen mai da ake haƙowa a kowace rana, wato ganga miliyan 1.6, naira ɗaya kuma daidai da dala ɗaya kuma naira 435 a farashin gwamnati a bankina.
Dattawan sun amince da kasafin kuɗin bayan da Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi, Sanata Barau Jibrin ya damƙa wa majalisa rahoton sa.
Rahoton kwamitin Barau dai ya antaya ƙarin naira 967 a ɓangaren da kasafin majalisar dattawa ke ciki.
Kasafin 2023: Za A Biya Bashin Naira Tiriliyan 6,557,597,611,797
Kasafin 2023: Ayyukan Yau Da Kullum: Naira Tiriliyan 8,329,370,195,637.
Kasafin 2023: Ayyukan Yau Da Kullum: Naira Tiriliyan 5,972,734,929,421.
A lokacin da ya ke sa wa kasafin hannu a ranar Talata, Buhari ya ce yana lura da canje-canjen da Majalisar Dattawa ta yi cikin kasafin na sa da ya tura masu.
Sannan kuma ya ce Majalisar Dattawa ta yi ƙarin kuɗaɗen ne saboda ta shigar da wasu sabbin ayyukan raya ƙasa ne da ta ke so a yi a faɗin ƙasar nan a cikin kasafin 2023.
Ya ce ayyukan da ta ƙara laftawa za su ci naira bilyan 770.72. Sannan kuma ta yi wa Ma’aikatu, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnatin Tarayya ƙare-ƙaren kuɗaɗe har Naira biliyan 58.55.
Sai dai kuma ya ce ya yi gaggawar sa wa kasafin hannu ne domin a samu a fara aiki da shi ba tare da wani jinkiri ba.
Discussion about this post