Babban mai baiwa kwamitin Kamfen ɗin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, Mahmud Jega ya bayyana cewa dama jam’iyyar APC na shirin korar Naja’atu Mohammed ne ta yi gaggawar sanar da ta fice daga jam’iyyar.
Jega ya ce ” Kwamitin na gab da kammala binciken bankaɗo wani sirri na ta da aka gano cewa ashe turo ta ka yi ta rika kai bayanan sirri ga PDP.
” Mun gano cewa ashe dai ita turo ta aka yi ta rika daukan bayanan APC ta na kai ma jam’iyyar adawa da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
” An kore ta ne saboda cin amana da yi wa jam’iyya da ɗan takarar mu zagon kasa. Asirinta ne ya tonu shine ta yi gaggawar kaucewa. Amma kuma mu korar ta zamu yi dama.
Discussion about this post