Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, a ranar Talata ya bayyana cewa wa’adin ranar 31 ga watan Janairu na nan daram,tsoffin kudi na N200, N500 da N1,000 za su daina aiki.
Da yake magana kan sabbin takardun kudin, Emefiele ya ce ida za a lura za a ga cewa sace-sacen mutane da karbar kudin fansa ya ragu tun lokacin da aka sake fasalin takardun kudin guda uku. Ya kuma kara da cewa, lokacin da aka bayar na musanya tsofaffin takardun kudi na Naira da sababbi ya isa ‘yan Najeriya su samu sabbin takardun daga bankuna.
” Yanzu dai bani da labari mai dadi ga wadanda ke so a kara swa’adin daina kashe tsoffin takardun kudi, Su yi hakuri ba za a kara wa’adin ba. Kowa ya garzaya ya canja kudin sa a banki.”
“Dalili kuwa shi ne domin kwanaki 90 (muna jin kwana 100) ya isa wadanda ke da tsohon kudin su ajiye su, kudaden, a bankuna. Kuma mun dauki kowane mataki don tabbatar da cewa dukkan bankunan sun bude don karbar duk tsoffin kudade. Kwanaki 100, mun yi imani, sun fi isa. ”
Sai dai kuma mutane da yawa har da gwamnoni sun koka kan dakatar da kashe wadannan kudade, suna cewa bankuna ba su bada sabbin kudin sannan kuma ma wasu ba su karbar tsoffin kudi.
Discussion about this post