Masu surutu su na yi, wasu su na aiki, lokaci kuma yana wucewa haka lamarin duniya yake faruwa wata rana kuma sai dai labari.
Amma a rayuwarka ka yi ƙoƙarin kasancewa a cikin mutane masu aiki domin cigaban Al’umma ba masu surutu ba akan manufofin gwamnati da bakasan irin alfanun dake cikinsa ba.
Kashi 99.9 na shugabanni a duniya suna kawo sabbin dokoki ne saboda masalahar al’ummarsu bawai domin su cutar da su ba. Baya ga batun tsaro da yaki da cin hanci da rashawa, hujjoji ke nan da gwamnati ta bayar a bayyane domin sauya fasalin takardun kudi.
Najeriya tana daya daga cikin kasashe Bakwai a duniya wanda ‘yan kasarta basa ajiya a asusun banki na zamani. Rahoton Bankin duniya mai suna ‘Globan Findex report’ na shekarar 2021, ya aiyana sauran kasashen kamar haka: China, India, Pakistan, Bangladesh, Indonesia da kuma Egypt.
A duniya baki daya akwai mutum biliyan 1.4 wadanda ba su ajiya a banki, ma’ana ba su da alaka da duk wata hanya ta hada-hadar kudi ta zamani wanda shi ne tushen gina tattalin arziki mai karfi.
Sai idan mutane suna ajiya a banki za’a iya auna karfin arzikinsu kuma ta haka masu zaba jari na kasahen duniya za su zo su kafa kamfanoni domin samarwa mutane aikin yi. Sun san cewa akwai arziki a kasar kuma.
Kididdigar masana ta nuna cewa yankin Arewacin Arewa ya fi kowanne yanki na Najeriya Talauci da Fatara kuma haka yana da alaka da rashin yin ajiya a asusun zamani na banki.
Ana amfani da kalmar Talauci ta hanyar tsorata masu zuba jari a arewa saboda mai arziki yafi son ya zuba jari a inda ake walwala da hada-hadar kudi.
A Najeriya Kashe 80 na bankuna yana hannun yan ƙabilar Igbo yan kasuwarsu masu kananan karfi kai tsaye suke samun lamuni domin ranto kudi wajen bunkasa kasuwancisu.
Arewa ba banki ko daya, Bank of the North a zamanin Charles Soludo, aka karya shi saboda bamu da karfin jari da kuma rashin masu ajiya a bankin.
Akwai arziki a Arewa amma Dan Arewa yana kwalliya da babu. Har ma za ka ji yana cewa arziki tsiraici ne sai da boyewa. Shi Dan Arewa a tunaninsa idan ya kai kudinsa banki, kamar ya bayyana sirrinsa sa ne shi ya sa ya gwammace ya boye kudinsa a gida. Harma ya mutu ba’asan a ina yake ajiya ba.
Wannan canjin kudin dama ce ga yan Arewa su fahimci zamani na Allah ne, dole mubi abinda zamani ya zo da shi matakur bai sabawa koyarwar addinin musulunci.
Akwai Bankuna na zamani masu bin tsarin kasuwanci irin koyarwar addinin musulunci, idan muka kai kudaden mu a nan zamu bunkasa tattalin arzikin Arewa mu kuma canza tunanin masu zuba jari cewar mu talakawa bamu da komai.
Ba dole bane sai kana da kudi ba zaka bude asusun banki na zamani. Ba’a taba samun gwamnati a Negeriya ba wanda ta taimakawa Talakawa da tallafin rage talauci ba irin wannan gwannatin ta Buhari. Amma taimakon gwamnati baya zuwa wajen talakawa wadanda basu da asusun ajiya a banki.
Dole Dan Arewa ya farka yaje ya bude asusun banki idan ya na so ya taimakawa kansa da kuma yankin Arewa. Ni tsohon dan Npower ne, tun da aka fara biya na kudin Npower a shekarar 2016 nayi adabo da kinko (Talauci) hakan ya faru saboda ina da asusun ajiya a banki.
Yau a garin Kano da kauyuka wadanda basu da asusun ajiya na banki su suka fi shan wahalar chanjin kudi, babu wani banki a Kano da ake bin layi domin ajiyar kudi, sai dai masu bude asusun ajiya ko masu ciran sabon Kudi. Duk wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani (Social Media) na yan siyasa ne da yan korensu masu neman cin zabe ta hanyar siyan kuri’a.
Ni nasan Shugaba Muhammadu Buhari ba zai kirkiro chanza kudi domin ya gallazawa talakawa ba. Dole muje mu bude asusun ajiya a banki domin mu taimakawa yankin mu na arewa.
Baba Habu Fagge Dan Jarida ne daga Jihar Kano