Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya bayyana cewa wajibi bankuna ne su gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe daga hannun jama’a, har bayan cikar wa’adin 10 Ga Fabrairu, 2023 ranar da ake rufe amfani tsoffin takardun kuɗaɗen N1,000, N500 da kuma naira N200.
Emefiele ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana gaban Kwamitin Majalisar Tarayya, inda ya yi magana dangane da tsare-tsaren da ke tattare da canjin kuɗaɗe.
Ya ce ya amince da Dokar Najeriya Sashe na 20(3) wanda ya wajibta wa Bankuna cewa su riƙa karɓar tsoffin kuɗaɗe har bayan wa’adin karɓar tsoffin kuɗaɗe.
Duk da cewa Emefiele ya yi bayani a ranar Lahadi ya bada sanarwar cewa a ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe har zuwa 17 Ga Fabrairu, amma su ‘yan majalisar tarayya ta ce kwanaki goman da aka ƙara sun yi kaɗan, kamata ya yi a ƙara watanni ba kwanaki ba.
“Ina bai wa ‘yan Najeriya cewa ba za su yi asarar kuɗaɗen su ba. Duk wanda bai rigaya ya kai kuɗin da banki ba, zai iya kaiwa ko da bayan 10 Ga Fabrairu. Za a ajiye masa, ko kuma ya yi hada-hada da su ta asusun sa na banki.”
PREMIUM Times ya buga labarin yadda Gwamnan CBN ya koma aiki ana tsakiyar jidalin sauyin kuɗi da jalli-jogar Gudaji Kazaure
Ranar Litinin ta mako biyu ne da rana an shiga dabur-dabur, yayin da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ya koma aiki a Hedikwatar CBN ɗin.
Ya koma aikin ne bayan ya shafe makonni baya Najeriya a cikin yanayi na rashin tabbas ɗin takamaimen abin da ya ke yi a Amurka.
Ya bar Najeriya a lokacin da ake cewa jami’an SSS na neman sa, sannan kuma ya koma ranar Litinin jim kaɗan sai wasu rahotanni su ka ce jami’an SSS sun mamaye Hedikwatar CBN, tare da hana kowa shiga cikin harabar a matsayin ma’aikatan bankin.
Sai dai kuma Kakakin SSS Peter Afunanya ya bayyana cewa rahoton karya ce, jami’an su ba su mamaye CBN ba, a ranar 16 Ga Janairu, 2023.
Cikin makon jiya ne PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Emefiele ya laɓaɓo, ya dawo Najeriya a asirce.
Majiya kuma ta ji cewa Emefiele ya shirya barin Najeriya kwanan nan, yayin da jami’an SSS ke neman kama shi.
An ce “zai tsare ya bar Najeriya ta yadda idan ya fita halartar Taron Tattalin Arziki na Duniya (WEF), to daga can ba zai dawo ba.”
Emefiele ya dawo yayin da ake shirin taron Kwamitin Tattauna Tattalin Arziki (MPC), wanda za a gabatar ranar 24 Ga Janairu.
Wannan taron tsare-tsaren dai shi ne zai magana a kan makomar jidalin da sauyin kuɗi da sauran matsalolin da su ka shafi tattalin arziki da kuma darajar Naira.
Abin da zai fi ɗaukar hankalin jama’a shi ne yadda za a ƙarke da Emefiele, dangane da zarge-zargen salwanta ko karkatar da tiriliyan 89 da Honorabul Gudaji Kazaure ya yi masa.
Discussion about this post