Bayan tir da kashe wasu jami’an Sibul Difens 7 da ‘yan baindiga suka yi a Kaduna Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Jami’an tsaro su gaggauta kamo su sannan su hukunta su.
Bayan haka shugaba Buhari ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan wadanda suka rasu a wannan harin kwantar bauna da aka kai musu a Kaduna.
Garba Shehu wanda ya fitar da sanarwar ya ce Buhari yayi matukar alhinin kisan wadannan dakaru da ‘yan bindiga suka yi.
jihar Kaduna na daga cikin jihohin Arewa Maso Yammacin Najeriya da hare-haren ‘yan bindiga suka yi tsanani. Kananan hukumomi irin su Birnin Gwari, Chikun, Giwa da Kajuru na fama da hare-haren ‘yan bindiga babu sassauci.
Discussion about this post