Kotun Ƙoli ya kori neman alfarmar da iyalan tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha su ka yi, inda su ka roƙi a dakatar da gwamnatin Najeriya ci gaba da ta ke yi na bankaɗo kuɗaɗen da su ka salwanta ko aka karkatar a zamanin mulkin sa.
Ɗan marigayi Abacha, wato Mohammed Abacha ne ya nemi kotun ta hana a ci gaba da bankaɗo kuɗaɗen satar da su ka salwanta ko aka karkatar da su.
Mohammed Abacha ya nemi Kotun Ƙoli ta hana a ƙwace wasu kadarorin su.
Kadarorin dai su na da alaƙa da wasu daga cikin iyalan Abacha, amma hukuma ta nemi iznin a garƙame su.
Ya Abacha ya yi mulki daga 1993 zuwa 1998.
Alƙalin Kotun Koli Emmanual Agim ne ya karanta hukuncin a ranar Alhamis, cewa hukuncin da aka ɗauka a tsayuwar farkon sauraron hukuncin ya yi daidai.
Agim ya kori ƙarar da iyalan na marigayi Abacha su ka kai, kuma ya umarci su biya kuɗin ɓata lokacin yin shari’ar da su ka yi.
Ƙarar dai kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar, ita ce mai lamba SC/641/2013, babban ɗan Abacha wanda ke raye, Mohammed Abacha ne ya shigar da ita, shi da wani wani ɗan mai suna Abba, a madadin kan su da sauran iyalan na Abacha.
Iyalan na Abacha dai sun kai ƙarar Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami, Sufeto Janar na ‘yan Sanda, DCP P.Y Hana wanda shi ne shugaban kwamitin bincike da wasu mutanen.
Idan ba a manta ba, an fara binciken iyalan Abacha tun cikin 1999, watanni kaɗan bayan rantsar da Obasanjo shugaban ƙasa na lokacin.
Discussion about this post