A ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi don hana ma’aikatan gwamnati dulmiya hannu a cikin kuɗaɗen gwamnati, Hukumar Bin Diddigin Fitar Kuɗaɗen Gwamnati (NFIU) ta haramta wa ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya, na jihohi da na ƙananan hukumomi zuwa banki su ciri kuɗaɗe niƙi-niƙi.
Babban Daraktan Hukumar NFIU, Modibbo Hamman-Tukur ne ya yi wannan sanarwa da gargaɗin, lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, ranar Alhamis, a Abuja.
Tukur ya ce, “daga ranar 31 Ga Fabrairu, 2023 an haramta wa kowane jami’in gwamnatin ko ma wane ne ya ciri kuɗaɗe daga asusun gwamnati ko asusun hukumar sa ko ma’aikatar sa ko cibiyar sa.
Ya ce dama can akwai dokar, haka kawai ake karya ta ƙiri-ƙiri a dukkan ma’aikatun ƙasar nan.
Ya ce, “Daga 2015 zuwa Satumba, 2022, a ciri naira tiriliyan 1 a asusun gwamnati, wanda hakan kuma karya doka ce muraran.”
Tukur ya ce ma’aikatan gwamanti su na tsoma hannayen su da ƙafafuwan su cikin harƙallar kuɗaɗe, ta hanyar cirar kuɗaɗe kai-tsaye a loda a fita da su daga banki.
Ya ƙara da tunatar da cewa Dokar NFIU Sashe na 3 (1) (a) – (s), ya haramta wa ma’aikatan gwamnati cirar kuɗaɗen da za a yi koma wane irin aiki da daga banki.
Tukur ya ƙara da bayar da hujja da abin da Sashe na 23 (2) na Dokar NFIU ya rattaba, a 2018.
Ya ce Shugaban Ƙasa ne kaɗai ke da ikon bai wa wani iznin ya ciri kuɗi niƙi-niƙi ya fita da su daga banki, idan har dalilin hakan ya zama tilas.
Discussion about this post