A ƙoƙarin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke yi don tabbatar da kowane ɗan Najeriya na amfani da asusun banki duk rashin nauyin aljihun sa, wato Financial Inclusion, an ƙaddamar da Katin Sauƙaƙa Hada-hadar Kuɗaɗe na Ƙasa.
Yayin ƙaddamarwar, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya ce wannan shiri wani sabon faifai ne da zai tabbatar da sauƙaƙa wa mutane hada-hadar kuɗaɗe a faɗin Najeriya.
“Zancen gaskiya ina matuƙar farin cikin ganin cewa Tsarin Tafiyar da Hada-hadar Bankuna zai ƙarfafa karɓa da biyan kuɗaɗe a hanyar Shirin Katin Sauƙaƙa Hada-hadar Kuɗaɗe, wato Domestic Card Scheme,” inji shi.
“Shirin Daina Hada-hadar Takardun Kuɗaɗe, wanda ya zaburar da kowane ɗan Najeriya wajen ganin ya na amfani da asusun ajiyar kuɗaɗe, ya fara ne tun a cikin 2012.
“Shiri ne wanda ya ƙarfafa hanyoyin hada-hadar kuɗaɗe ta hanyar amfani da na’urori, ba tare da ana jidar kuɗaɗe niƙi-niƙi ba a Najeriya.
“A kan haka ne CBN ya haɗa guiwa da sauran masu ruwa da tsaki wajen ingantawa da ƙarfafa tsarin Lambar Tantance Mallakar Asusun Ajiyar Banki (BVN), RTGS, SANEF, RS da irin su tsarin alaben eNaira.”
“Shi wannan tsarin Katin Sauƙaƙa Hada-hadar Kuɗaɗe na Cikin Ƙasa, zai yi gogayya da katin Visa da Mastercard na ATM.”
Shi dai Katin Sauƙaƙa Hada-hadar Kuɗaɗe na Ƙasa zai yi amfani ne har a wuraren da babu bankuna.
Kuma katin zai rage yawan dogaro da amfani da kamfanonin ƙasashen waje wajen samar mana da tsarin hada-hadar kuɗaɗe na zamani.
An dai ƙaddamar da wannan sabon sabon tsari a ƙarƙashin Tsarin Hada-hadar Bankuna na NIBSS, tare da haɗin guiwa da Kwamitin Bankuna na Najeriya.
Emefiele ya ce an ƙirƙiro shirin ne, saboda har yanzu mutane da dama a Najeriya ba su amfani da asusun ajiyar banki, duk kuma da ɓullo da katin ATM da P.O.S ɗin da aka yi.
“Saboda haka wannan kati zai kasance kowane ɗan Najeriya ya mallake shi, musamman domin sauƙaƙa hada-hadar kuɗaɗe a cikin ƙasa da yankunan karkara.”
Discussion about this post