Gwamnatin Tarayya ta ƙara tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ko kaɗan ba za a ɗaga zaɓen 2023 ba, zai gudana kamar yadda aka tsara.
Ministan Yaɗa Labarai da Inganta Al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a wurin bajekolin bayanan ayyukan da Buhari ya yi wa Najeriya, daga 2015 zuwa 2023.
INEC dai ta tsara cewa za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da majalisar dattawa da mambobin tarayya, a ranar 25 Ga Fabrairu, sai kuma zaɓen gwamnoni a ranar 11 ga Maris, duk a cikin shekarar wato a cikin farkon shekarar nan.
Wani da ya yi magana a madadin INEC wurin wani taro, .ai suna Abdullahi Ziri ne ya nuna cewa matsalar tsaro ka iya sa a ɗage zaɓen 2023.
Sai dai kuma Lai ya ce kowa ya kwantar da hankalin sa, baza a ɗage zaɓen 2023 ba.
“Duk wani da aka san ya na da hannu a wajen harkokin zaɓe, ya na bakin ƙoƙarin ganin cewa an gudanar da zaɓen 2023 bisa tsari na kwanciyar hankali, wanda babu wani rikici.
“Gwamnatin Tarayya ba ta yi tunanin ɗage zaɓe, za a yi shi a ranar da aka tsara.
Zuru wanda ya ce zaɓen 2023 na fuskantar barazana, shi ne Shugaban Hukumar Gudanarwar BEI, hukumar Kula da Harkokin Zaɓe.