Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya ce a yanzu a ƙasar duk zalamar mutum bai isa ya yi wa zaɓe maguɗi ba.
Akeredolu ya ce shigo da tsarin na’urar tantance adadin waɗanda su ka yi rajistar katin zaɓe ya sa mutum ba zai iya jefa kuri’a ba, idan ba shi da katin rajista, sannan kuma ba zai iya jefa ƙuri’a sau biyu ko fiye da haka ba.
Wannan na’ura dai wato BVAS, Akeredolu ya ce abin alfahari ce kuma abin alheri wajen tsaftace tafarkin dimokraɗiyya a ƙasar nan.
An shigo da amfani da BVAS ne a cikin Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022.
Gwamna Akeredolu ya yi wannan bayani lokacin da ya karɓi baƙuncin Kwamishinan Zaɓe na Ƙasa da aka tura Jihar Ondo, mai suna Rufus Akeju.
Daga nan gwamnan ya jinjina wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), saboda namijin ƙoƙarin da hukumar ta yi wajen ƙirƙiro tsarin zaɓe ta hanyar amfani da BVAS, na’urar da bai yiwuwa ta bari a yi maguɗin zaɓe.
Ya yi kira ga INEC cewa ta samar da hanyoyin da jama’a za su riƙa karɓar katin shaidar rajistar su, ba tare da shan wahala ba.