Shugaban jam’iyyar APC na jihar Yobe, Mohammed Gadaka, ya gargadi masu tunanin yiwa jam’iyyar zagon kasa (anti-party) a babban zaben 2023, inda ya bukaci su canja tunani, saboda uwar jam’iyyar ba zata lamunta da take-taken wasu yan siyasa ba, a shirye take wajen kare muradun jam’iyyar a karkashin Gwamna Buni, wajen yakar masu kokarin kawo cikas da rarrabuwar kan yan jam’iyyar, a kowane mataki, musamman lokacin da ake tunkarar babban zaben 2023.
A cikin sanarwar manema labaru mai dauke da sa-hannun Hajiya Sa’adatu Maina, Sakatariyar Yada Labaru a ofishin shugaban jam’iyyar APC na jihar Yobe, Alhaji Gadaka, ta ce ya yi wannan gargadin ne ranar Laraba, a sa’ilin da yake karbar kimanin mutum 1488, a karkashin jagorancin Alhaji Rama, wadanda suka canja sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a unguwar Dogo Tebo dake garin Potiskum a jihar Yobe.
Bugu da kari kuma, shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa shugabancin APC ba zai rungume hannu ya na kallo wasu tsiraru suna yunkurin yiwa jam’iyya zagon kasa ba; ya ce lokaci yayi wanda ba za su bari hakan ya faru ba ta hanyar taka musu burki.
“Mun ga abin da ya faru a yau, yayain da daruruwan jama’a suka yo tururuwa zuwa jam’iyyar mu. Kuma ita harkar jam’iyya ko siyasa ba ruwanta da shekararka dari a cikinta, ko wane yau ya shigo. Kuma ko shakka babu a matsayin ka na dan jam’iyyar APC, a karkashin gwamnatin Gwamna Buni, an yi maka halascin da ya kamata amma daga baya ka zo ka ce ba a yi maka yadda kake so ba, kuma zaka ci amanar jam’iyyar. Nayi imanin kana zolayar kanka ne, domin dukanmu da muke a nan babu wanda yake da karfin iko irin na gwamnati, kuma irin ta adalin Gwamna Mai Mala Buni; ya ba kowa hakkinsa kuma ya rike kowa bisa amana.”
“Saboda haka idan kace zaka ci amanar Gwamna, ka ci amanar jam’iyya, to mu kuma muna shalanta maka cewa: kowaye kai idan ka ce zaka ci amanar jam’iyyar ba zamu kyaleka ba. Kuma idan kana tunanin zaka yi duk abin da kake so, saboda ka san Gwamna mutum ne mai sassauci. To kowa ya shirya, kuma ku gaya musu cewa zamu bi dasu ta kofar da suka shigo. Zamu yi abin da ko shi Mai Girma Gwamna ba zai ce me yasa ba.”
Hajiya Sa’adatu Maina ta kara da cewa, shugaban jam’iyyar APC, Alhaji Mohammed Gadaka ya bayyana cewa ya kwashe sama da shekara 30 yana amintaka da Gwamna Buni, ya ce, “Na san Gwamna Buni a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana wanda kowane lokaci burinsa shi ne sauke amanar da ya dsuka.”
“Sannan a matsayinmu na wadanda muke zaune tare dashi zaman amana, saboda haka duk wanda ya taba jam’iyyar APC ya taba mu kai tsaye, kuma ba zai yuwu mu yarda wani ya zuba mana kasa a ciki ba; zamu yakeka da duk abin da bai sabawa doka ba, kuma zamu yi amfani da dukiyarmu, da duk karfinmu wajen kare muradun jam’iyyar APC a kowane mataki. Zamu yi duk abin da ya dace wajen samun gagarumar nasarar jam’iyyar APC a kowane mataki, zamu yi tsayin dska da dukan karfinmu wajen kare muradun Gwamna Buni a karkashin jam’iyyar APC a jihar Yobe da Nijeriya baki daya.”
Mohammed Gadaka ya jaddada cewa, idan akwai wani tsageran da ya isa, a shirye uwar jam’iyyar APC take ta fafata dashi a dimukuradiyyance don nuna misa cewa shi ba kowa ne a jihar Yobe. Sannan kuma mu nunawa duniya cewa jihar Yobe gidan jam’iyyar APC ce, kuma jam’iyya mafi karfin fada aji a kasashen Afrika.”
A karshe, shugaban jam’iyyar APC ya yiwa daruruwan magoya bayan jam’iyyar godiya bisa hadin kan da suke bai wa uwar jam’iyyar tare da kira karesu su ci gaba da zama tsintiya madaurinki guda, su yi kokari wajen hada kai da yan uwansu wadanda suka shigo jam’iyyar ba tare da nuna bambanci ba. Kuma ya bukaci wadanda suka sauya sheka da cewa su dauka daga yau halastaccin yan jam’iyyar APC ne ba su da bambanci da wanda ya shekara 100 a ciki.
Discussion about this post