Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, a ranar Laraba ya yi zargin cewa ana shirin yin magudi a babban zaben kasar.
A ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris ne za a gudanar da zabukan na tarayya da na jihohi.
Amma yayin da yake jawabi a babban filin wasa na Moshood Abiola International Stadium, Abeokuta, jihar Ogun, Tinubu ya ce akwai wasu da ke kokarin ganin ba a yi zabukan a wadannan rana ba, wato suna son su kawo cikas ga zabukan.
Tinubu ya ce karancin man fetur da ake fama da shi a fadin kasar nan da kuma sake fasalin kudin Najeriya wato Naira na daga cikin shirin yi wa zaben zagon kasa.
Sai dai ya tabbatar wa magoya bayansa, wadanda dubbansu suka halarci gangamin, cewa ba za a iya hana wannan zabe ba ko nasarar sa a zaben ba.
Wannan zabe gwagwarmaya ce, kuma jihadi, za mu karbi mulki daga hannunsu, ba sa son a yi zabe, amma ba za mu yarda ba, suna son fakewa da karancin man fetur don haddasa rikicin ta yadda za a samu. ba za a yi zabe ba,” in ji Tinubu.
Ko da man fetur ko babu, za mu yi zabe. Ba tare da man fetur ba, za mu yi zabe. Kun san ni sosai, za mu yi nasara, za mu karbi ragamar mulki daga hannunsu. Za mu hadu aii a ranar zabe.
Manyan jiga-jigan APC a jihar duk sun halarci taron gangamin da suka hada da tsohon gwamnan jihar Gbenga Daniel, tsohon kakakin majalisar tarayya, Dimeji Bankole da dai sauran su.
Discussion about this post