Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana sanarwar tsige Kwamishinan Harkokin Addinin Musulunci, Tahir Adamu, wanda aka fi sani da ‘Baba Impossible’.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Muhammad Garba ne ya bayyana wa manema labarai haka a ranar Asabar.
1 – Garba ya ce an cire shi ne saboda halayen rashin biyayya ga Gwamna Ganduje da kuma karya doka.
2 – Sai kuma furta kalamai ba tare da yi wa bakin linzami ba.
Garba ya ce an tsige Baba Impossible nan take.
3 – “An tsige shi ne saboda ya bijiro da wasu halaye waɗanda sun ci karo da irin ɗabi’un ma’aikacin gwamanti wanda ke riƙe da ofishi irin na sa na al’amurran addinin Musulunci,
4 – Da kuma sakin bakin sa babu linzami da ya ke yi idan ya na maganganu.” Inji Garba.
5 – Sannan ya ƙara da cewa an tsige kwamishinan saboda an gano ya na amfani da ofishin, ya maida shi hanyar sa ta cimma kasuwancinci da neman kuɗi.
6 – Kuma ya yi gaban-gabarar rage wa ma’aikatan ofishin sa ranakun aiki, ya sa su ka daina zuwa ofis a ranakun Laraba da Juma’a.
7 – Nan take aka bada sanarwar naɗa Nazifi Ishaq a madadin sa.
‘Baba Impossible’ dai tsohon malamin Jami’ar Bayero ne, a Kano. Shi ma Ishaq da aka maye gurbin sa da shi, malami ne a Jami’ar Bayero.
Dukkan su biyu ɗin mabiya ɗariƙar Tijjaniya ne.
Gwamnatin Ganduje Maƙaryaciya Ce – ‘Baba Impossible’:
Sai dai kuma a raddin da ya maida jim kaɗan bayan jin sanarwar tsige shi, Tahir Adamu ya ce gwamnatin Kano maƙaryaciya ce, inda ya ce ya kai takardar sauka daga aiki kwana ɗaya kafin a yi sanarwar tsige shi.
Discussion about this post