Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Mohammed ya rasu.
Santurakin Dutse, Lamido Mustapha ya sanar da rasuwar a madadin masarautar Dutse.
Ya ce, Sarki Nuhu ta rasa a Abuja ranar Talata.
Taƙaitaccen tarihin marigayi Nuhu Mohammed, Sarkin Dutse
Mai martaba Sarkin Dutse ya yi shekaru ashirin da takwas akan kujerar mulkin al’ummar ƙananan hukumomin Dutse, Kiyawa, Birnin Kudu, Buji, Gwaram, Jahun da Miga, Sunan sa na yanka Nuhu, sunan mahaifinsa Muhammadu Sunusi.
An haife shi a garin `Ƴargaba, yanzu shekarunsa 78 da haihuwa sannan ya zama sarki yana da shekaru 50 a duniya, matansa 2, ƴaƴansa 13, 9 daga cikinsu mata ne guda 4 maza ne.
Karatun sa
Marigayi sarki Nuhu ya na da MBA a jami’ar Ohio a shekarar 1974, Allah ya hore masa ilmin Arabiyya ya kuma haddace Al-Qur’ani. Jami’ar gwamnatin tarayya ta Owerri ta bashi digirin girmamawa, shine uban jami’ar gwamnatin jihar Sokoto daga shekarar 2014 zuwa yau, shugaban Najeriya ya bashi lambar girmamawa ta ƙasa mai daraja ta huɗu (Commander Order of Niger) yayi tafiye-tafiye a ƙasashen duniya.
Masarautarsa tana da yawan hakimai masu gari (ƙasa) guda 28 da suka fito daga ƙananan hukumomi 7, yawan hakimai marasa ƙasa guda 58 da akwai dagatai 356 a ƙarƙashinsa waɗanda su ma suka fito daga ƙananan hukumomin da suke masarautar, akwai masu unguwanni da yawansu ya kai 2,082 a ƙarƙashin mulkinsa na adalci.
A zamanin mulkinsa ne garin Dutse ya tashi daga ƙauye zuwa karkara, ya zama birni, sannan garin ya taɓa zama zakaran gwaji da yafi kowanne babban birnin jiha tsafta a Nijeriya a shekarar 2012, kuma ya zama ɗaya daga cikin garuruwan da suka fi kowanne gari ci gaba a nahiyar Afrika.
Yayi fice a wajen tattara zakkah da rabawa a cikin sarakunan Najeriya, an bashi lambobin yabo na ciki da wajen Jigawa a fannin sulhu da sasanta al’ummarsa, ya gina masallatai da islamiyyoyi domin ƴaɗa addinin Allah.
Discussion about this post