Dan takarar Gwamnan jihar Kebbi a karkashin jami’yyar PDP Aminu Bande a ranar Litini ya fara kamen dinsa da yin alkawarin cewa yana da kwarewar da zai iya kawo ƙarshen rashin taro a jihar fiye da abokin takarar sa na jami’yyar APC, Nasiru Idris.
Bande wanda ya kai matsayin manjo-janar a aiki soja a Najeriya kafin ya yi ritaya ya ce abokin takarar sa na APC, wato Idris bashi da kwarewar da zai kawo ƙarshen rashin tsaro a jihar saboda shi malamin aji biyu ne.
Idan ba a manta ba Idris wanda ke rike da shugabancin kungiyar malamai ta kasa NUT ya zama dan takarar Gwamnan jihar ne bayan zaben fidda gwanin da jami’yyar APC ta gudanar a watan Mayun 2022.
” Ba za a iya kwatanta kwarewar soja mai muƙamin manjo-janar da na malamin aji biyu ba saboda horon da na samu lokacin da nake aikin soja ba na wasa bane, shi ne ya sa nake da kwarewar da zan iya kawo ƙarshen rashin tsaro a jihar.
“ Ya ƴan jihar Kebbi, na yi muku alkawarin samar da takin zamani kafin damina yazo a farashi mai sauki Idan kuka zabe ni gwamna.
Bande ya kuma ce inganta ilimin boko na daga cikin mahimman abubuwan da yake so ya gyara a jihar.
“Matasan mu na gararamba saboda rashin aikin yi. Ya kamata mu gyara makarantun mu yadda dalibai za su iya koyan sana’o’in hannu domin inganta rayuwar su.
“Za mu Yi haka ta hanyar farfado da makarantun koyon sana’o’in hannun da muke da su.
“Ku kula da wadanda za su zo su yi muku romon baki da kudade domin su siya kuri’un ku ku karbi kudaden domin na ku ne amma kada ku zaɓe su.
Tohon gwamnan jihar Adamu Aleiro da tsohon Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Abdullahi Yahaya wadanda a kwanakin baya suka canja sheka daga jami’yyar APC zuwa PDP na daga cikin manyan ‘yan siyasan da suka halarci taron.
Aleiro ya yi kira ga mutane da su zabi Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa, sannan su zaɓi Bade gwamnan jihar Kebbi.
“ Saboda matsalolin rashin tsaro ya sa mutane ke neman canjin a mulkin kasar nan kuma ku sani dan takarar Shugaban kasa Atiku Abubakar na da kwarewar da zai iya kawo karshen rashin tsaro a kasar nan.
Ya ce a zaben da za a yi bana mutanen jihar Kebbi ba za su bari a sace musu kuri’un su ba.
“Ranar zabe kada ku jefa kuri’ar ku ku tafi gida ku tsaya domin tabbatar da cewa an kirga kuri’un a idanuwanku domin akwai ‘yan siyasan da basu kamfen sai dai su jira yin murɗiya.
“Kada ku basu dama su sace kuri’un ku. A jihar Kebbi bana ba za mu bari a yi magudi a zabe ba. Za mu hada hannu da hukumar zabe domin ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a jihar.
Discussion about this post