Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani Bamuwa Umaru mai shekaru 62 da laifin baiwa jami’an tsaro cin hanci har Naira miliyan daya.
Kakakin rundunar Abdullahi Kiyawa ya ce rundunar ta kama Umaru ranar 16 ga Disambar 2022 a karamar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna.
Kiyawa ya ce Umaru ya bayyana wa Shugaban fannin dake kama masu garkuwa da mutane Aliyu Mohammed cewa zai biya shi naira miliyan daya idan har zai saki wani Aliyu Mohammed da rundunar ta kama bisa laifin yin garkuwa da mutane.
“Jami’an tsaron dake aiki a ofishin Rijiyar Zaki ne suka kama Yusuf Ibrahim mai shekara 27 daga kauyen Danjibga dake karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara a tashar motocin dake Rijiyar Zaki a Kano.
“Jami’an tsaron sun kama Ibrahim bayan wani direba a tashar motocin da suka yi garkuwa da shi a hanyar Funtuwa zuwa Gusau ya gane shi.
“Direban ya biya naira 500,000 kafin suka sake shi.
Kiyawa ya ce Ibrahim ya bayyana wa jami’an tsaron cewa gungun su masu sace mutane ne ke yin garkuwa da mutane a kauyukan Sheme, Yankara, Askari da Kucheri a jihohin Katsina da Zamfara.
“Ibrahim ya kuma ce sun kashe akalla mutum 10 daga cikin yawan mutanen da suka yi garkuwa da su inda shi ya kashe mutum biyu ne kawai a tsawon sana’ar garkuwa da mutane da ake yi.
Ya ce rundunar za ta Kai wadannan mutane kotu da zarar ta kammala gudanar da bincike akan su.
Discussion about this post