Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama Gaddafi Sagir da ya kashe kishiyar mahaifiyar sa Rabiatu Sahir da ‘Sukudireba’ sannan ya shake ƴarta ya murɗe ta sai da ta mutu a unguwar Rijiyar Lemu dake jihar Kano.
Kakakin rundunar Abdullahi Kiyawa ya shaida cewa mahaifin Gaddafi ne ya kawo kara ofishin ƴan sanda inda ya sanar musu cewa ya dawo gida ya iske matar sa da ƴar sa kwance cikin jini male-male.
Kiyawa ya kara da cewa ” Bayan mahaifin Gaddafi wato Sagir ya kawo kara ofishin ƴan sanda, ya sanar mana cewa yana zargin ɗan sa da aikata wannan mummunar abu.
” Ko da aka kai su asibitin Murtata sai likitoci suka tabbatar mana cewa da matar mai suna Rabi’atu da ƴarta Munawwara duk sun rasu.
Da muka kama Gaddafi, sai ya tabbatar mana cewa shine ya kashe su, bayan sabani da ya shiga tsakanin su da wannan mata.
Gaddafi ya ce ” Da na dawo gida zan danki abinci, sai matar mahaifina wato kishiyar mahaifiyata ta rufe ni da faɗa, daga nan sai muka kaure da kokuwa. Ni kuma sai na ciro ‘Sukudireba’ na rika caka mata a kai har sai da ta dai na numfashi.
” Ita kuma ƴar ta wato Munawwara, ta hau duka na da muciya, daga nan ita ma na kamata na shaƙe ta da wani zani a wuya har sai da ta dai na numfashi.
Gaddafi ya roki sassauci daga ƴan sanda yana mai cewa ba zai sake aikata irin haka ba.