Shugaban hukumar hana Sha da fataucin muggan kwayoyi NDLEA Mohammed Marwa ya bayyana cewa a cikin watanni 24 hukumar ta kama masu fataucin muggan kwayoyi har 24,458 a kasar nan.
Ya ce manyan dillalen kwayoyi guda 34 na daga cikin yawan masu da hukumar ta kama a tsakanin wannan lokaci.
Marwa ya fadi haka ne a taron da ya yi da namema labarai ranar Laraba a Abuja.
Ya ce kotu ta yanke wa mutum 3,733 hukunci daga cikin mutum 24,458 din da hukumar ta kama.
Marwa ya ce hukumar ta Kuma kula da mutum 19,401 dake fama da matsalolin da suka fashi zaucewa da tabuwar hankali a dalilin ta’ammali da kwayoyi.
Ya yi kira ga mutane da su rika kula da mutanen da suke hulda da su musamman wadanda ba su tabbatar da aiyukkan da suke yi ba.
Marwa ya ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kama duk masu fatauci ko sha muggan kwayoyi a kasar nan.
“A dalilin kokarin da hukumar ta yi an kama manyan dillalen muggan kwayoyi da a yanzu haka za a hukunta su bisa ga laifin da suka aikata.
Ya yi gargadi ga masu fatauci da Shan muggan kwayoyi da su nemi sana’ar yi tunda wuri domin duk wanda hukumar ta kama ba za a daga masa kai ba.
Discussion about this post