Kungiyar cigaban mutanen garin Chawai da ke karamar hukumar Kauru Abel Adam ya sanar da sace Hakimin garin Chawai Joshua Ahmadu ranar Laraba.
A takardar wanda ya sakawa hannu ya ce ƴan bindigan sun shiga harin Chawai da misalin karfe 9:45 na dare.
Kungiyar ta ce ko da maharan suka dira gaein sun zarce ne kai tsaye zuwa gidan hakimin sannan suka arce da shi.
” Muna so mu sanar wa mutane cewa lallai kungiyar CDA za ta yi duk abinda za ta yi wajen ganin an ceto wanda aka sace. Sannan muna kira ga ƴan kabilar Tsam su taya mu da addu’a a sako basaraken.
Bayan haka kungiyar ta yi kira ga matasa masu ƴan bijilanye dake sintiri a garin su maida hankali kwarai wajen ganin irin haka bai auku ba.
” Ya dai kamata matasa su maida hankali wajen samar da tsaro a yankin. Da sun maida hankali kwarai da irin haka bai auku ba.
Kamfanin dillanci labaran Najeriya NANta ruwaito cewa rundunar ƴan sandan yankin Kafanchan sun ziyarci iyalan Hakimin kuma sun tattauna da su gabani fara bincike akan wannan hari.
Karamar hukumar Kauru na daga cikin kananan Hukumomin da ƴan bindiga suka addaba a jihar Kaduna musamman yankin Chawai da wasu garuruwa dake kargashin karamar hukumar.