Jam’iyyar APC a ƙarƙashin Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu, ta bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar ba abin bai wa amanar riƙon Najeriya ba ne.
Kakakin Kamfen ɗin TInubu, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Abuja, a ranar Lahadi.
Onanuga ya ce kamata ya yi NDLEA ta kama Atiku Abubakar ta bincike shi dangane da zargin harka da muggan ƙwayoyi da aka yi masa a cikin wani faifan murya da aka watsa a makon jiya.
Haka kuma ya yi kira ga EFCC ta gayyaci Atiku Abubakar dangane da zargin harƙallar maƙudan kuɗaɗe da duk dai wani mai suna Micheal Achimugu ya yi wa Atiku.
Achimugu ya shafe makonni biyu ya na watsa bayanan da ke ɗauke da zarge-zargen harƙallar da ya ce Atiku ya yi a lokacin da ya ke Mataimakin Shugaban Ƙasa, tsanakin 1999 zuwa 2007.
Achimugu ya yi iƙirarin cewa ya taɓa yin aiki a hannun Atiku, a matsayin hadimin Mataimakin Shugaban Ƙasa.
Idan ba a manta ba, ita ma jam’iyyyar PDP ta zargi Bola Tinubu, ɗan takarar APC da haifin harƙalla da muggan ƙwayoyi a cikin 2015.
Kusan manyan jam’iyyun guda biyu dai, wato PDP da APC sun saki layin kamfen kan alherin da za su shuka idan aka zaɓe su, sun karkata zuwa ga kamfen ɗin yarfe kan ‘yan takarar su na shugaban ƙasa, wato Atiku Abubakar na PDP da kuma Bola Ahmed Tinubu na APC.