Kwamitin Majalisar Tarayya ya ce kwanaki goman da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya ƙara kan ci gaba da canjin kuɗi, sun yi kaɗan, kuma rainin wayau ne.
Shugaban kwamiti Honorabul Ado Doguwa ya ce tilas Emefiele ya dokar Najeriya, ko kuma su sa a kama shi.
Ya ce tilas Emefiele ya bi Sashe na 20 na Dokar CBN, ko kuma ya fuskanci fushin majalisa.
A ranar Lahadi ce Emefiele ya yi sanarwar ƙarin wa’adin kwanaki 10, bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a Daura.
Yanzu a cewar sa, za a daina karɓar tsoffin kuɗaɗe a ranar 10 Ga Fabrairu.
Bayan haka idan ba a manta ba Wani lauya mai suna Joshua Alobo, ya maka Babban Bankin Najeriya (CBN) kotu, inda ya nemi kotu ta soke wa’adin ranar 31 Ga Janairu da CBN ya bayar, a matsayin ranar daina amfani da tsoffin nairori.
Alobo, wanda farfesa ne a fannin lauya da shari’a, ya nemi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke ranar da CBN ta bayar, wato 31 Ga Janairu a matsayin ranar daina karɓar tsoffin kuɗaɗe.
Discussion about this post