Dan takaran Gwamnan jihar Katsina na jami’yyar PRP Imran Jino ya yi alkawarin kawar da matsalolin rashin tsaro da bunkasa tattalin arzikin jihar Katsina idan ya yi nasarar zama gwamnan jihar Katsina a 2023.
Jino ya fadi haka ne a hirar da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a garin Katsina ranar Laraba.
“ Ina kira ga mutane da su zabi shugabannin na gari dake da kwarewar da za su samar da ci gaba da inganta rayuwar mutane a jihar.
Ya ce zai kawar da matsalolin da suka addabi jihar ta hanyar inganta ilimin boko, kiwon lafiya, aiyukkan noma, muhalli, tsaro, samar wa matasa aikin yi, haraji da dai sauran su.
“ Ina kira ga sarakunan gargajiya, malaman addini da masu fada a ji da su wayar da kan mutane sanin mahimmancin zaben shugabanni na gari a lokacin zabe.
Jino ya kara yin kira ga mazauna karkara da su zabi shugabanni na gari da za su tuna da su bayan sun ci zabe su rika bin su hargida suna bibiyan halin da suke ciki domin cigaban su.
Discussion about this post