• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Gwamnatin Zamfara ta zargin tsohon gwamna Matawalle da sace motocin gwamnatin jihar da wasu kayan gwamnati

    Gwamnatin Kano ta rusa katafaren bene mai hawa uku da aka yi bisa filin gwamnati da Ganduje ya raba wa ƴan uwa da abokan arziki

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    TSAUTSAYI: Yadda ‘yan bindiga suka ware da Lami Awarware da Haulatu bayan halartar taron rantsar da Uba Sani a Kaduna

    Sojojin Najariya sun kara ragargaza wa Boko Haram motocin yaki bakwai

    Sojoji sun dagargaza matatun mai 47 sun kama barayin mai 65 – Hedikwatar tsaro na kasa

    HAJJI 2023: Yadda jirgin maniyyatan Jigawa ya koma Kano ba shiri, bayan ya samu matsala cikin sararin samaniyar Kamaru

    GANAWAR TINUBU DA NLC: Ƙungiyar Ƙwadago ta ce a tilas a soke ƙarin kuɗin mai, an shammaci ‘yan Najeriya

    Buhari-signing-2020-budget

    Gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari ta sanar da sabbin nade-nade a daidai ana rantsar da Tinubu shugaban kasa

    Minista Sadiya ta miƙa ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai ga Babban Sakatare

    2015-2023: ‘Na yi sukuwa ta lafiya, na kai zamiya lafiya’ – Buhari

    BANKWANA DA BUHARI: ‘Tinubu yau mafarkin ka ya zama gaskiya, Allah ya sa ka kai Najeriya fiye da inda na kai ta’ – Nasihar Buhari ga Asiwaju

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

ZAMFARA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Fiye da ƴan bindiga 100 ne bama-baman Sojojin Sama ya hallaka

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
December 21, 2022
in Labarai
0
Jiragen sojojin saman Najeriya sun yi wa maboyar hatsabibin ɗan bindiga luguden bamabamai a Kaduna

Rahotanni sun nuna cewa hare-haren bama-bamai da Sojojin Saman Najeriya su ka kai yankin Malele Matumji a Massrautar Ɗansadau ya halaka fiye da mutum 100.

Jaridar PR Nigeria mai kusanci sosai ga hukumomin tsaron ƙasar nan, ta ruwaito cewa an tsakanin ‘yan bindiga da fararen hula, an kashe mutum 270.

Yayin da Rundunar Sojojin Najeriya ba su ƙaryata labarin ba, jaridar ta ci gaba da cewa maharan sun kashe Sojojin Najeriya 10.

PREMIUM TIMES a ranar Litinin dai ta bada rahoton kisan mutum 64.

Majiya ta shaida wa wakilin mu cewa waɗanda aka kashe a cikin fararen hula a ƙauyukan Matumji da Malele sun fi mutum 100.

“An kashe ‘yan bindiga a Malale za su mai 26. A Matumji kuwa an kashe ‘yan bindiga 68, waɗanda su ka yi ƙoƙarin tsere wa rugugin wutar bama-baman sojoji.

Wani da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce “yan bindiga sun mamaye Malele ne da niyyar kashe duk wani abu mai rai a ƙauyen. Sun yi niyyar ba za su bar kowa da rai ba. Saboda shekaru da dama sun yi ta ƙoƙarin mamaye ƙauyen, amma ba su samu nasara ba.

“Shi ne a wannan karo su ka wo gayyar dangin su daga ƙasashen waje cikin Afirka, da nufin su ragargaza ƙauyen baki ɗaya.” Haka Nuhu Ɗansadau ya shaida wa wakilin mu.

Kakakin Sojojin Sama ya shaida wa wakilin mu cewa nan ba da daɗewa ba zai fitar da sanarwa ga manema labarai dangane da ƙarin hasken da zai yi. Amma bai bayyana adadin sojojin da aka kashe, yawan ‘yan ta’adda ko adadin farashin hular da wannan ƙazamin yaƙi ya ritsa da su ba.

Gwamnatin Jihar dai ta fitar sanarwar ta’aziyya da jajentawa ga iyalan fararen hular da yaƙin ya ritsa da rayuwar su.

Bayanan farko kafin wannan ƙarin haske dai sun nuna cewa bama-baman Sojojin Sama ya halaka ‘yan bindiga da fararen hula 64, a yankin da gogarma Lawali Damina ya yi garkuwa da mutum 270.

Da farko labarin ya nuna cewa harin da Sojojin Saman Najeriya su ka kai wa ‘yan ta’adda a ƙauyen Mutumji ya yi sanadiyyar kashe ‘yan bindiga da dama, tare da fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba.

Harin bama-baman ya faru ne kwana ɗaya bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda gogarma Lawali Damina ya yi garkuwa da ilahirin mazan cikin ƙauyen Randa, ƙauyen da ke ƙarƙashin mazaɓar Mutumji.

Sojoji sun kai harin ne bayan mazauna yankin sun yi masu kiran gaggawar shaida masu cewa ‘yan bindiga sun darkaki ƙauyukan Malele, Ruwan Tofa da ‘Yan Awaki.

Majiya ta ce sojojin sama ɗin sun daƙile kai farmakin, inda mahara su ka tsere cikin garin Mutumji.

Sojojin Sama sun bi su da ruwan bama-bamai, inda lamarin ya ritsa har da fararen hula da dama.

Wani jami’i kuma mamba na Hukumar Kare Haƙƙin Jama’a, Nuhu Ɗansadau, ya shaida wa Premium Times cewa an kashe ‘yan ta’adda da fararen hula kamar 64. Sannan kuma waɗansu mutum 12 sun ji raunuka.

Ya ce a ranar Litinin an garzaya da waɗanda su ka ji raunukan zuwa Gusau domin ci gaba da kulawa da su.

Wani basarake a Mutumji mai suna Abdulƙadir Abdullahi, ya ce, “Gaskiya lamarin ya yi muni ƙwarai, domin har yanzu ana ci gaba da nemo gawarwakin wasu da ake nema ba a gani ba.

Fashi, Garkuwa Da Kashe-kashe A Ƙaramar Hukumar Maru:

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ɗan bindiga ya kwashe mazan gari guda, fiye da mutum 270 saboda faɗa kan budurwa, 20 sun mutu saboda ƙududun takaici da bugun zuciya.

Tantagaryar ɗan iskan ɗan ta’adda mai suna Lawali Damina, ya yi garkuwa da ilahirin mazajen ƙauyen Randa arankatakaf, har da yara ƙanana, saboda ɓatan bindigogin sa biyu bayan an yi rikici kan wata budurwa.

Ƙauyen Randa wanda ke cikin Mazaɓar Matumji a Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar Zamfara, ya na ƙarƙashin Masarautar Ɗansadau.

Mazauna yankin da kuma wani basarake da ke Matumji, sun shaida wa wakilin mu cewa asalin rikicin dai wani ɗan bindiga ne ke soyayya da wata baƙuwa mai suna Zaliha, wadda ta je ƙauyen daga wani gari wajen Shinkafi.

“To ranar da abin ya faru, ɗan bindigar ya shigo Randa, sai ya samu wasu ‘yan bindiga su biyu tsaye tare da Zaliha. Bayan sun yi sa-in-sa a tsakanin su, sai saurayin yarinyar mai suna Gora ya fusata, ya koma cikin daji. Ashe ya yi kwanton-ɓauna a hanya, sai da waɗancan ‘yan bindigar su ka zo wucewa, sai ya bindige su biyun kuma ya tsere. Dama kuma ba cikin rundunar waɗanda ya kashe ɗin ya ke ba.

Yadda Kisan Yaran Lawali Damina Ya Zame Wa Mazauna Randa Balbalin Bala’i:

“Yayin da gogarma Lawali Damina ya samu labarin an kashe yaran sa biyu, ya je har Randa ya tilasta wa mazauna garin cewa su yi wa gawarwakin biyu sallah, kuma su bizne su a maƙabartar garin.

“Bayan an rufe su, Damina ya dawo shi kaɗai, ya tara ilahirin mazan Randa babba da yaro, su ka taru ƙarƙashin wani mangwaro a bayan gari, ya ce masu ya yafe kisan yaran sa biyu, amma duk inda aka kai bindigogin su biyu, to a fito masa da su.

“Mutanen garin ba su san ‘yan bindiga na kewaye da su a cikin daji ba, yayin da su ka ce lallai ba su ɗauki bindigogin ba, sai Damina ya kira su, duk aka kwashe gaba ɗayan mazan garin babba da yaro ƙarami, fiye da mutum 270.” Inji dagacin Matumji, Abdulƙadir Abdullahi.

Rayuwar Mazan Randa 270 A Hannun Gogarma Lawali Damina:

Abdullahi ya shaida wa wakilin mu cewa daga cikin sama da mutum 270 da aka yi garkuwa da su, 20 sun mutu, saboda irin rayuwar ƙunci da takurar da su ka yi a wani ɗan ƙaramin wurin da aka ɓoye su.

“Wasu bala’in baƙin ciki da ƙududun damuwa ya kashe su, wasu yawan jini, wasu bugun zuciya, wasu kuma tsananin firgita ce, saboda a kan idon su sun ga an gigara wa ɗaya daga cikin takobi, aka yi masa yankan rago.” Inji Abdullahi.

Ya ƙara da cewa Damina ya ce tunda ba a fito masa da bindigogin biyu ba, to sai an biya diyyar Naira miliyan 60 sannan ya saki kamammun.

Abin Da Ke Kai ‘Yan Bindiga Cikin Ƙauyen Randa:

Ƙauyen Randa ya kasance a ƙarƙashin kulawar ɗan bindiga Lawali Damisa. Mutanen ƙauyen su na biyan shi ‘harajin daina kai masu hari’. Su kuma ‘yan bindigar su na shigowa ƙauyen su yi duk harkokin da su ke so da mutanen garin.

PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kwamishinan Harkokin Tsaro na Jihar Zamfara, Mamman Tsafe, wanda ya ce a ba shi awa ɗaya zai kira wakilin na mu.

Majiya ta ce har zuwa haɗa wannan rahoton Gwamnatin Zamfara ba ta yi wani hoɓɓasa ba.

Tags: AbujaHausaLabaraiZamfara
Previous Post

ZAƁEN 2023: INEC za ta yi amfani da ma’aikata miliyan 1, motocin sufuri 100,000, jiragen ruwa 4,200 – Yakubu

Next Post

Hukumar Hisbah ta kama mutum 19 da suka halarci daurin auren wasu maza biyu, Abba da Mujahid a Kano

Ashafa Murnai

Ashafa Murnai

Next Post
Kano Hisbah

Hukumar Hisbah ta kama mutum 19 da suka halarci daurin auren wasu maza biyu, Abba da Mujahid a Kano

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Yadda bashin Dala Miliyan 95 na Bankin Musulunci ya bunƙasa noma a ƙananan hukumomin Kano 44 – Hamisu, Kodinetan KSADP
  • Gwamnatin Zamfara ta zargin tsohon gwamna Matawalle da sace motocin gwamnatin jihar da wasu kayan gwamnati
  • Gwamnatin Kano ta rusa katafaren bene mai hawa uku da aka yi bisa filin gwamnati da Ganduje ya raba wa ƴan uwa da abokan arziki
  • TSAUTSAYI: Yadda ‘yan bindiga suka ware da Lami Awarware da Haulatu bayan halartar taron rantsar da Uba Sani a Kaduna
  • Gwamnatin Kano ta hana lika fastoci a ginegine a fadin jihar

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.