Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu masoya da suka kashe jaririn da suka haifa saboda ba su shirya haihuwa ba.
Kakakin rundunar Lawan Adam ya sanar da haka a garin Dutse a farkon wannan mako.
Adam ya ce idan rundunar ta kammala bincike za ta kai masoyan kotu domin yanke musu hukunci.
Ya ce rundunar ta kama Balaraba Shehu mai shekara 30 a kauyen Tsurma dake karamar hukumar Kiyawa ranar biyu ga Disemba da misalin karfe 11:50 na safe.
Rundunar ta kama Balaraba wacce ta haka rami ta birne jaririn da ta haifa bayan karar da aka kawo ofishin ‘yan sandan.
“ Bayan an kawo mana labarin haka sai muka yi gaggawar zuwa kauyen inda muka hako jaririn daga ramin da aka birne shi sannan muka kama Balaraba.
“ Mun kai jaririn babban asibitin Dutse inda likita ya tabbatar cewa jaririn ya rasu amma ita Balaraba na tsare a ofishin mu.
“Rundunar ta kuma kama wani Amadu Sale wanda aka fi sani da ‘Dan Kwaito’ mai shekaru 25 Kuma mahaifin jaririn a kauyen Akar dake karamar hukumar Kiyawa.
Adam ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Emmanuel Ekot Effiom ya ce fannin dake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka zai ci gaba da yin bincike akai.