Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu sun kama wani boka Emmanuel Odoh mai shekaru 23 a kauyen Umuaram dake garin Ikem karamar hukumar Isi-Uzo bayan ya kashe wani kwostoman sa Onunze Benedict lokacin gwajin lakanin bindiga.
Bokan Odoh ya kashe Benedict a kauyen Eha-Amufu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Daniel Ndukwe ya ce rundunar ‘yan sandan dake Isi-Uzo ne suka kama bokan ranar 26 ga Nuwamba.
Ndukwe ya ce ‘yan sandan sun kama bindiga kirar ‘Double Barrel’ na hannu guda daya a tare da bokan.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga wani labari makamancin haka wanda ya auku a jihar Kwara.
A Kwara, wani matashi ne ya kashe Kanin sa a lokacin gwajin lakanin bindiga da suka karbo wurin wani boka.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Ajayi Okasanmi ya ace wan ya kashe kanensa mai shekara 12 lokacin da suke gwajin lakanin bindiga dawani boka ya basu.
Bayan yaran sun karɓo lakanin ssai wan ya dauko bindigar da mahaifinsu mai suna Abubakar Abubakar, ke zuwa farauta da shi ya danƙara masa harsashi ya fuskanci ƙaninsa wanda shine ya ɗaura shirgegiyar layar da boka ya basu ya dirka masa ita.
Nan ko take kanen na sa ya yanke jiki ya faɗi gawa ko shureshire bai yi ba. Daga ganin haka kuwa sai wan ya tattara nasa-inasa ya arce.
Okasanmi ya ce matashin ya kashe kanensa a Dutse Gogo dake karamar hukumar Kaiama.
Ya ce tuni rundunar ta fara farautar matashin domin hukunta shi.