A kotun dake sauraron kararrakin cin zarafin mata da yara kanana dake Ikeja jihar Legas ne wata matar likita mai suna Aderemi Faleye ta faɗi yadda mijinta likita Femi Olaleye ya rika bata maganin barci tdomin ya rika samun damar yin lalata da ƴar kanwan sa da ke zama da su.
Adeyemi ta ce tun wannan yarin ya tana shekara 16 ne Femi ya fara lalata da ita. A shekara mai zuwa zata cika sheka 18 da haihuwa.
Kotu ta gurfanar da Femi bisa laifukan da suka hada da cin zarafi da fyade sannan kotun ta bashi beli bayan ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa a kai.
Adeyemi ta auri Femi shekaru 11 da suka wuce sannan suna da ya’ya biyu namiji mai shekara 10 da mace ‘yar shekara 7.
Aderemi ta ce mijinta kulum da dare ya kan bata magani ‘junior aspirin’ da ‘Phenergan’ wanda idan ta sha suke sata ta yi barci mai nauyi.
Aderemi ta ce da ya bata maganin sai su kwanta amma ashe shi yana farkawa wajen karfe biyun dare ya koma ɗakin yarinyar ya yi lalata da ita it kuma ta na ta sharɓa bacci.
Ta ce mijinta ya fara yin lalata da yarinyar ta hanyar nuna mata fina-finan batsa yana saka azakarinsa a cikin bakin yarinyar har ya zuba maniyinsa a baki.
Aderemi ta ce asirin mijinta ya tonu a ranar da yarinyar ta yi wa mai aiki rashin kunya inda aka nemi a ladabtar da ita amma Femi ya hana kuma ya kai ta ajiya gidan kanwan Aderemi.
“Kanwan Aderemi ta lallashi yarinyar inda ta fada mata yadda Femi ke lalata da ita har ta dubura.
Ta ce a ofishin ‘yan sanda Femi ya tabbatar wa ‘yan sanda cewa lallai ya yi lalata da yarinyar.
Aderemi ta ce mijinta ya fara lalata da yarinyar daga Maris 2020 zuwa Nuwanba 2021.
A watan Disemba 2022 Femi ya Kai kansa asibitin kula da masu fama da jirkicewar kwakwalwa inda likitan mai sun Ogunnubi ta bayyana wa Aderemi cewa Femi na fama da matsalar jirkicewar hankali sannan idan ba a nemi magani ba zai iya zama babban matsala ga rayuwarsa da wadanda ke kusa da shi.
“Idan har Femi zai iya yin lalata da ‘yar kanwansa dake kiran da baba zai iya yin lalata da ‘yar cikinsa.
Discussion about this post