Abin ɓoye ya fito fili, domin tabbatattun bayani na nuna cewa a ranar 9 Ga Disamba, Hukumar SSS ta garzaya Babbar Kotun Tarayya, inda ta nemi a ba ta sammacin iznin kamo Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, amma kotun ta ƙi.
Shugaban Alƙalan Babbar Kotun Tarayya ne, Babban Mai Shari’a John Ɗantsoho ya ƙi amincewa da roƙon da SSS ɗin su ka yi, bisa ga dalilin cewa sun kasa bai wa kotu gasasshen dalili ko hujjar kama Gwamnan Babban Bankin na CBN.
SSS dai sun shigar da ƙarar neman sammacin kama Emefiele a wasiƙar da su ka aika wa Babbar Kotun Tarayya, mai lamba FHC/ABJ/CS/2255/2022, wanda Ɗantsoho ya yi zama kan buƙatar ta SSS a Babbar Kotun Tarayya mai Lamba 7 Abuja.
SSS dai sun bayyana cewa su na son su damƙe Emefiele “domin bincikar sa kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci, harƙalla, laifin karya tattalin arzikin ƙasa da kuma laifukan da su ka shafi muhimmin al’amarin tsaron ƙasa.”
Mai Shari’a Ɗantsoho ya ƙi amincewa, bisa dalilin cewa ba a fito takamaimai an bayyana laifukan da ya yi har ake zargin sa ba. Ma’ana, a cewar SSS ta bai wa kotu ba’asi a ƙudundune.
“Sannan kuma SSS ba su bayyana shin wane Godwin Emefiele su ke neman a ba su sammacin kamawa ba. Sun dai rubuta Godwin Emefiele kawai.
“To in dai Godwin Emefiele Gwamnan CBN su ke nufi, matsayin sa na mai riƙe da tasarifin kuɗin Najeriya, kama shi sai da sanin shugaba.”
Hakan dai na nufin ba zai yiwu a kama Emefiele ba sa sanin Shugaba Muhammadu Buhari ba kenan.
Emefiele dai ya bi Shugaba Muhammadu Buhari zuwa Amurka kwanaki biyu da kotun ta hana a damƙe shi.
Yayin da ya ke shan suka kan taƙaita adadin kuɗaɗen da za a iya cira ta ATM da POS zuwa naira 20,000 kacal, ana zargin sa cewa ya kasa yin komai dangane da faɗuwar darajar Naira, inda sai da ta kai har naira 740 a kssuwar ‘yan canji.
Haka kuma Da Majalisar Tarayya Gudaji Kazaure na zargin sa salwantar da naira tiriliyan 89 na harajin stamp duty.
A gefe ɗaya kuma, yau Talata ce Shugaba Buhari ya kulle ƙofa ya yi ganawar sirri da Gbajabiamila.
A ranar Talata ɗin nan ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri tare da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila.
Shugabannin biyu dai sun gana ne kan batun tsarin taƙaita cirar kuɗi zuwa naira 20,000 kacal a kullum da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Goodwin Emefiele ya ƙirƙiro da amincewar Buhari.
Bayan ganawar ta su, Gbajabiamila ya shaida wa manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa cewa, “mun tattauna batun Gwamnan CBN Godwin Emefiele, da kuma batun zaɓen 2023, wanda mu ka tattauna batun hanyoyin kauce wa tashen-tashen hankula lokacin zaɓe. Mun kuma tattauna wasu batutuwa daban-daban.
Buhari da Gbajabiamila sun gana ne a ranar da Emefiele ya ƙi zuwa amsa gayyatar da Majalisar Tarayya ta yi masa, domin zuwa ya yi bayani kan tsarin taƙaita cirar kuɗi zuwa naira 20,000.
Dama kuma Majalisa ta umarce shi da ya dakatar da aiwatar da tsarin taƙaita cire kuɗaɗen.
Manema labarai sun tambayi Gbajabiamila dangane da zargin da Ɗan Majalisar Tarayya Gudaji Kazaure ke wa Gwamnan CBN cewa kuɗaɗen harajin stamp duty sun salwanta a hannun sa har naira tiriliyan 89, sai Gbajabiamila ya ce Gudaji shi kaɗai ke kiɗan sa, ya ke rawar sa, ba da yawun Majalisar Tarayya ya ke yi ba.
Discussion about this post