Ƙungiyar cigaban umasarautar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna sun yi korafin cewa ƴan siyasa sun yaudare su da cika musu baki a duk lokacin da aka buga gangar siyasa suka zo neman kuri’u a yankin.
Shugaban Kungiyar BEPU Ishaq Usman ya bayyana cewa ” Mutanen yankin Birnin Gwari sun gaji jin gafara ga shanu nan, amma ko ƙaho ba su gani ba.
” Nan a 2015 lokacin Kamfen El-Rufai ya zo ya rika cika mana baki cewa wai idan ya zama gwamna zai maido da fadar gwamnatin jihar kacokan zuwa Birnin Gwari domin a kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da yankin ke fama da shi. Amma babu abinda aka yi shekaru 7 kenan sai tsananin wahalar rashin tsaro da mutane suka yi ta fama da.
” Yanzu ne dai muke ɗan samun sauki saboda tsananta buɗe wuta da ake yi wa ƴan ta’addan dake yankin.
Kungiyar ta kara da cewa abu biyu ne suke bukatar Tinubu ya yi musu alkawarin samar musu idan ya zama shugaban kasa kafin su bashi kuri’un su.
” Na farko shine samar da tsaro da farfaɗo da harkokin kasuwanci a yankin wanda suka daɗe suna fama da shi. Sai kuma gyara manyan titunan da suka haɗa Birnin Gwari da garin Kaduna da kuma wanda ya haɗa garin da Funtua.
Usman ya ce waɗannan sune wasu daga cikin muhimman ayyukan da suke so Tinubu ya sani yakuma yi musu alƙawain cikawa idan ya zama gwamna.
Tinubu ya ziyarci masarautar Birnin Gwari domin kai ziyarar ban girma ga sarkin Birnin Gwari, Maimartaba Zubairu Jibrin Maigwari II.
Bayan haka masarautar ta naɗa Tinubu sarautar Dakaren Birnin Gwari.