Rundunar ƴan sanda jihar Borno ta kama masu tada zaune tsaye a jihar sama da mutum 500 daga Janairu zuwa Disambar 2022.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abdu Umar ya sanar da haka a garin Maiduguri.
Umar ya ce rundunar ta saurari kararraki 636 a cikin wannan shekara inda kotu ta saurari kararraki 372 daga ciki sannan ta yanke wa mutum 314 hukunci.
Ya ce daga cikin mutum 314 din da kotu ta yanke wa hukunci akwai mutum 102 da aka kama da laifin fyade, mutum 200 ‘yan bindiga, mutum 57 kisa, mutum 22 ‘Yan fashi da makami da mutum 30 masu garkuwa da mutane.
Saura sun hada da mutum 11 masu yi wa mutane barna, 28 masu safarar muggan kwayoyi, mutum 138 barayi, da kuma mutum 3 masu safarar mutane.
Rundunar ta Kuma damka mutum shida hannun sojin Najeriya, NSCDC, NDLEA da dai sauran su saboda laifin da suka aikata.
Kwamishinan ya ce rundunar ta kama bindigogi kirar hannu 12, AK-47 3, bom kirar grenade daya, bindiga kirar RPG hudu, harsashin bindiga mai tsawon milimita 7.62 2,950, da bindiga kiran Pump Action guda uku.
Sauran kuwa sun hada da barandami daya, adda, wukake da takubba 108, kwaya Exol 410, fakitin kwayoyin tramadol 21 da baka guda 12.
Umar ya ce rundunar ta mayar wa mutane kayan su da waɗannan ɓarayi suka sace da suka hada da
motoci, Keke NAPEP, na’urar POS, na’urar Sola inverter da sauran su.
Bayan haka Umar ya mika godiyarsa ga gwamnatin jihar karkashin gwamnana jihar Babagana Zulum bisa baya da rundunar ke samu.