Kafin tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi Umaru ‘Yar’Adua ya tsige Nuhu Ribadu daga shugabancin EFCC cikin 2007, sai da jajirtaccen mayaƙin rashawa da cin hancin ya samu kyakkyawan yabo da jinjina daga tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, wanda ‘Yar’Adua ya gada.
Kwanaki uku bayan saukar Obasanjo daga mulki a ranar 29 Ga Mayu, 2007, sai ya rubuta wa Ribadu wasiƙar jinjina masa bisa yadda ya yi aikin sa a EFCC ba sani ba sabo. Ya rubuta masa wasiƙar a ranar 1 Ga Yuni, 2007.
Obasanjo ya fassara Ribadu a matsayin wani namijin zakin da bai san tsoro ba.
Wannan wasiƙar ta na cikin tulin wasiƙun sirrin da ke ƙunshe cikin littafin da Babban Editan PREMIUM TIMES, Musikilu Mojeed ya wallafa, wanda aka gabatar a ranar 1 Ga Nuwamba, 2022, mai suna ‘THE LETTERMAN’, wato KUNDIN WASIƘUN SIRRIKAN OBASANJO.
“Ya kai Nuhu Ribadu, ina yi maka yabo da jinjina na musamman, saboda jajircewar da ka ke yi wajen yaƙi da rashawa da cin hanci, a shugabancin da ka ke yi a EFCC. Ina yi maka godiya ta musamman, domin ka ma cancanci na kira ka sojan ƙwarai,” haka Obasanjo ya yabi Ribadu a cikin wasiƙar.
Ribadu ya yi shugabancin EFCC daga 2003 zuwa 2007. A lokacin sa EFCC ta yi suna wajen damƙe manyan shugabanni, musamman gwamnonin da su ka sauka daga mulki, lokacin da wa’adin kariyar su ya ƙare.
Kada a manta, Ribadu a matsayin sa na shugaban EFCC kuma Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, ya kama Sufeto Janar na ‘Yan Sanda a lokacin, Tafa Balogun, ya kulle shi, kuma ya ƙwace bargar motoci daga hannun sa.
A cikin wasiƙar har yau, Obasanjo ya nuna wa Ribadu cewa ya yi shirin fuskantar sabon ƙalubale, domin ya na da yaƙinin cewa sabon shugaban ƙasa na lokacin, Yar’Adua, zai ci gaba da aiki da shi.
Sai dai kuma ba a daɗe da yi wa Ribadu wannan jinjina ba, sai ‘Yar’Adua ya tsige shi, kuma ya rage masa muƙami.
An maye gurbin sa da Farisa Waziri, cikin 2008.
Bayan a tsige Ribadu daga shugabancin EFCC, ya fuskanci matsin-lambar da sai da ta kai ya yi gudun hijira ya bar Najeriya.
Discussion about this post