Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa a yanzu ciniki ko ribar ɗanyen mai da gas ɗin da Najeriya ke fitar ba za su iya riƙe Najeriya ba.
Dalilin haka ne tsohon shugaban ƙasar ya yi kira da a tashi haiƙan a bai wa harkar noma, musamman noman kasuwanci muhimmanci.
Obasanjo ya ce ‘yan Najeriya sun yi yawan da dogaro da kuɗin fetur ko gas ba zai fitar da ƙasar daga talauci, ƙuncin rayuwa har ta bunƙasa ba. Ya ce dole sai an tashi tsaye an bai wa harkar noma muhimmancin da za a maida shi hanyar samar wa ƙasar nan kuɗin shiga.
Da ya juyo kan zaɓen 2023, Obasanjo ya yi kira da kada a sa son zuciya wajen zaɓe, gudun kada a yi zaɓen-tumun-dare.
Tun farko da ya ke jawabi, Shugaban Ƙungiyar ta MUT, mai suna Orbee Ihagh, ya ce sun kawo wa Obasanjo ziyara domin su kwashi tubarraki a wurin sa a matsayin uba, uban ƙasa, jagora kuma dattijo mai hangen nesa, wanda ke kishin ƙabilar Tivi.
Obasanjo ya yi wannan batu ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin wata ƙungiyar kishin ƙabilar Tivi, mai suna Mzough U Tiv (MUT), waɗanda su ka kai masa ziyara a gidan sa da ke Otta, Jihar Ogun a ranar Lahadi.
Ko a cikin 1999 ma sai da Obasanjo ya ce wajibi ne Najeriya ta rungumi harkar noma gadan-gadan, ta daina dogaro da kuɗin fetur da gas.
Shugaban Ƙabilar na Tivi, ya ce su na goyon bayan mulki ya koma kudu a zaɓen 2023, domin a riƙa yin adalci bisa tsarin karɓa-karɓa, yadda su ma ‘yan ƙabilar Tivi za su karɓi mulkin Najeriya a shekarar 2031.
Yawan Jama’a A Najeriya Sun Kai Yawan ‘Yan Ƙasashen Afrika 32:
Har yanzu dai babu takamaiman adadin ƙididdigar yawan ‘yan Najeriya, duk da dai ana ta ƙiyasin cewa an haura mutum miliyan 200.
Wata ƙididdigar yawan al’ummar ƙasashen Afirka wanda PREMIUM TIMES HAUSA ta yi, ya tabbatar da cewa adadin yawan ‘yan Najeriya sun kai adadin yawan jama’ar wasu ƙasashen Afrika 32, waɗanda su ka haɗa da:
Seychelles, Sao Tome, Cape Verde, Comoros Insland, Djibouti, Eswatini, Equatorial Guinea, Mauritious, Guinea-Bissau, Gabon da Gambiya.
Sauran ƙasashen sun haɗa da Lesotho, Botswana, Namibiya, Liberiya, Jamhuriyar Kongo, Mauritania, Afrika ta Tsakiya, Libya, Togo da Saliyo.
Sauran ƙasashen sun haɗa da Eritrea, Sudan ta Kudu, Burundi, Jamhuriyar Benin, Ruwanda, Guinea, Tunisiya, Chadi, Zimbabwe da Malawi.
Discussion about this post