• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    2015-2023: ‘Na yi sukuwa ta lafiya, na kai zamiya lafiya’ – Buhari

    BANKWANA DA BUHARI: ‘Tinubu yau mafarkin ka ya zama gaskiya, Allah ya sa ka kai Najeriya fiye da inda na kai ta’ – Nasihar Buhari ga Asiwaju

    Tsakanin Sanata Barau da Gwamna Ganduje, Daga Jaafar Jaafar

    Ba zan jira Litinin ba, tun Lahadi zan mika mulki ga Abba Gida-Gida in kama gaba na – Ganduje

    RANTSAR DA TINUBU: Kotun Koli ta yi watsi da karar rashin cancantar Tinubu shiga zaɓen 2023

    RANAR RANTSAR DA TINUBU: Za mu hana makiyaya karakaina da shanu a cikin Abuja – Shugaban Miyetti Allah

    An Karrama gidan Jaridar PREMIUM TIMES da kyauta mafi daukaka a aikin Jarida na kasar Amurka

    BA DA MU BA, TAYA ƁERA ƁARI: PREMIUM TIMES ta nesanta kan ta daga ƙungiyar da ta jona sunan ta a shirya taron karrama wasu mutane

    KIRAN RUWA: ‘Ka wa Allah ka ɗaga mana kafa, kada ka kwace mana filayen mu har 9 da ka kunno kai a kan su – Makarfi ga El-Rufai

    ‘Ni da Wike kaman ‘Yan biyu ne, muna tsage gaskiya komai dacin ta’ – El-Rufai

    SABODA TIWITA: Sanatocin PDP sun fice daga Zauren Majalisar Dattawa

    Zaɓaɓɓun Sanatocin Arewa ta Tsakiya sun nemi a ba su Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ko a-yi-ta-ta-ƙare

    KIDAYA: An kashe naira biliyan 200 wurin shirye-shiryen fara ƙidayar jama’a – Shugaban Ƙidaya

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

TAKAZZA: Daga Ɓarnar Ruwa zuwa Zubar da Jini, Daga Dr Nuruddeen Muhammad

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
December 15, 2022
in Ra'ayi
0
TAKAZZA: Daga Ɓarnar Ruwa zuwa Zubar da Jini, Daga Dr Nuruddeen Muhammad

Takazza da ke yankin Ƙaramar Hukumar Guri ta Jihar Jigawa – kasancewarsa gari ne da ba sananne ba kuma wanda dalilai irin na yanayin muhalli, gurɓataccen shugabanci da rashin kyakkyawan wakilci suka ɓoye shi daga idon duniya – wani misali ne na irin mummunan halin da al’ummomi da dama suka sami kan su ciki a Shiyyar Arewa Maso Gabas ta wannan jiha. Bayan watanni uku kacal da farfaɗowar Takazza daga mummunar ɓarnar da ambaliyar ruwa ta haddasa, a yanzu haka al’ummar wannan gari suna fuskantar barazanar tashin hankali data jawo zubar da jini sakamakon farmakin da wasu mahara suka kai garin inda suka rusa gidaje da dama tare da yin awon gaba da dabbobin jama’a.

Ba na jin akwai wata al’umma a wannan yanki wadda ta shiga cikin matsanancin hali irin wanda al’ummar kauyen Takazza ta sami kanta a ciki a halin yanzu ba. A hankali ƙaunar wanna gari sai ƙara shiga raina take. Sau biyu ina mu’amala da mutanen garin a cikin watan Satumba na wannan shekara.

Da farko dai mutanen garin ne su ka yi tattaki zuwa gu na domin neman agaji na fatun buhuna da za su yi amfani da su wajen yin katanga ga ambaliyar ruwa da ta ke neman mamaye ɗan abin da ya rage daga gidajen ƙauyen. Domin kuwa tuni ruwan ya gama lalata dukkan amfanin gonar da suka shuka inda hatta maƙabartar da suka binne magabatansu a ciki sai da ruwan ya zaizaye ta kuma ya tone ƙaburburan.

A karo na biyu kuwa – kwanaki kaɗan bayan na farko – ya kasance mai cike da haɗari da kasadar ban mamaki. Mutanen ƙauyen ne suka buƙaci in kai ziyara garin don jajajantawa da yin musabaha da su. Nan take kuwa na amince da wannan buƙata ta su inda a ƙoƙarin hakan na shafe kusan awa guda cikin kwale-kwale ina tafiyar kasada akan ruwa mai zurfin gaske ba tare da ina ɗauke da kowane irin nau’i na kariya ba (wannan wani labari na daban).

Wahala da zaman ƙunci sun zama tamkar wani ɓangare na rayuwarmu a wannan yanki na arewa; saboda mun yarda sun zama jiki a garemu. Bugu da ƙari kuma addini da al’ada sun horas da mutanenmu kan juriya da ɗaukar ƙaddara a halin tsanani da wahala. Amma duk da hakan ban san lokacin da na fara zubar da hawaye ba lokacin da wasu magidanta biyu suka nuna mini daidai wurin da ruwa ya tafi da ‘ya’yansu ‘yan kwanaki kaɗan kafin zuwa na garin lokacin ambaliyar da aka yi a farkon watan Satumba. A dai wannan rana ce babban Limamin Takazza ya shafe awa guda cikin tsohon kwale-kwale yayin da ake ƙoƙarin tsallakar da shi zuwa gaɓa bayan ya kamu da matsananciyar rashin lafiya. Sai dai kuma Allah bai ƙadddara dawowarsa garin ba. Daidai faɗuwar rana labarin rasuwarsa ya iske mu a lokacin muna shirin kama hanyar komowarmu gida. Ƙalilan ne daga cikin mutanen Takazza suka halarci jana’iza ko yin ban kwana da gawar limaminsu da suke matuƙar girmamawa, domin kuwa a can kan tudu aka binne shi saboda babu halin dawo da gawar gida a rufe ta.

A halin yanzu, al’amarin da ya faro daga ‘yan ƙananan faɗace faɗace a gonakin Takazza da kewaye tsakanin manoman da suke ƙoƙarin alkinta ɗan abin da ya rage na amfanin gonarsu bayan ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi da kuma makiyaya waɗanda dabbobinsu suke matuƙar buƙatar abinci, ya fara rikiɗewa zuwa babban rikici. An yi kaca-kaca da gidajen jama’a tare da samun munanan raunuka inda hakan ke yin barana ga zaman lafiya (wanda ya haddasa kwashe mata da yara daga yankin a karo na biyu cikin watanni uku) saboda mabambantan dalilai guda biyu amma masu alaƙa da juna.

Gamayyar abubuwa irin su talauci, karancin ilmi, taɓarɓarewar muhalli da sha’anin siyasar koma-baya sun tilasta wa mutanenmu yin saranda da miƙa wuya. Amma, Alhamdu lillahi, an fara samun matakai na wayewar kan al’umma, sanya ido da kuma shiga a dama da su cikin al’amuran al’umma. Fatima Hajiya Gana Muhammad, haifaffiyar ƙauyen Takazza ce wadda kuma ta ke aikin Bautar Ƙasa a Jihar Kaduna. Tana cike da ɓacin rai lokacin da muka yi magana da ita. Abin da ya ɓata mata rai shine cewa a daren jiya samari ‘yan sa-kai da suka zo daga maƙwabtan ƙauyuka ne kaɗai (ba wai ‘yan ƙungiyar sintiri ba) suka riƙa tunkarar maharan suna korar su, koda yake nan take maharan suke sake komowa su kawo wani sabon farmakin. Shi ma Hassan Takazza ransa a ɓace yake. Wani mai suna Mallam Wada daga ƙauyen Damegi, wanda ke maƙwabtaka da Takazza, ya shaida mini cewa ana zaman ɗar ɗar a yankin yayin da aka girke jami’an kwantar da tarzoma da safiyar nan. Duk da haka ya ce har yanzu a cikin firgici yake. “Muna buƙatar ƙarin jami’an tsaro,” in ji shi.

Yayin da wataƙila akwai ƙamshin gaskiya a batun da ke cewa yawan tashin hankali da ake samu a yankunan ƙananan hukumomin Guri da Kirikasamma rigingimun yanki ne da aka jima ana yin su, toh haka ma kuma fa a bayyane yake cewa yanzu rikicin ya ƙara tsanani da faɗaɗa fiye da yadda yake a baya. Ana amfani da mugayen makamai inda hakan ke ƙara yawaitar mutanen da a ke kassarawa a rikicin. Har ila yau, yanayin harkokin tsaro na ƙasa baki ɗaya da kuma sauran al’amuran da ke kawo ɓaraka za su iya haɗuwa su zamar da yankunanmu masu fadama wuraren rikici da tashin hankali, idan har muka cigaba da nuna halin ko-in-kula da nuna damuwa a fatar baki saboda kawai wasu dalilan siyasa da ba sa kan ƙa’ida.

Akwai buƙatar mu yi la’akari da yiwuwar cewa wannan rikicin da muke ganin cewa ba wani abu ba ne zai iya rikiɗewa a gabanmu muna gani (Allah ya kiyaye), ya zama wani rikici da zai haɗa da manyan ma su laifi, muggan makamai da kuma haɗin bakin shuwagabanni da ba su san aikinsu ba. A ƙasa da watanni biyu da suka wuce, an sace tare da fille kan wani soja da ke bakin aiki a cikin yanayin da yake a zahiri ta’addaci ne!

Kamar sauran garuruwan da suke yankin Fadamar Haɗeja, halin da Takazza ke ciki wani abin lura ne idan ana nazarin alkinta arzikin ƙasa. Ga shi dai Allah ya azurta yankin da wadataccen ruwa, albarkatun dazuzzuka da kuma kyakkyawar ƙasar noma wadda ba a cika samun irinta ba, don haka babban abun da ya kamata mu sanya a gaba shine cewa mu sake salo da tsarin da muke gudanar da siyasa da al’amuran mulkin mu domin su riƙa tafiya daidai da wannan arziki da AllahSWT ya yi ma na; domin gudun kar arziki ya kuma zama tsiya (kamar yadda ake gani a wasu wurare masu yawan gaske). Ba yadda za a yi mutane su yi hasarar dukkan abubuwan da suka mallaka (gonaki, dabbobi, gidaje) a ambaliyar ruwan da ake iya kare faruwarta sannan kuma a lokaci guda su kasa samun zaman lafiya gami da hasarar rayukansu a hannun mahara ‘yan ta’adda!

A zuwa gaba, ya zama wajibi mu sake yin duba da nazari kan tsarin tsaronmu na cikin al’umma don ƙarfafawa tare da ingnta shi. Mu kuma ƙarfafa dokokin da ake da su yanzu domin a iya aiwatar da su yadda ya kamata. Haka zalika, sha’anin mulki da wakilcin jama’a su kasance ana yin su bisa gaskiya, ilimi da kuma ƙwarewa.

Haƙiƙa, hanyoyin shawo kan yawaitar ambaliyar ruwa da kuma yawan faruwar al’amura na rashin tsaro wanda suke faruwa sakamakon canjin yanayi, samuwar albarkatun dazuzzuka, kyakkyawar ƙasar noma da kuma ruwa, za su buƙaci wata sabuwar al’ada ta siyasa da kuma kwarewar da za ta iya kai wa ludayin mu kan dawon tanade tanaden harkokin tsaro da kare muhalli a matakin ƙasa da ma duniya baki ɗaya.

Dr Nuruddeen Muhammad shi ne Ɗan Takarar jam’iyyar PDP na mazaɓar Sanatan Arewa Maso Gabas a Jihar Jigawa sannan tsohon Ƙaramin Minista ne a Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje da kuma Ministan Watsa Labarai.

Tags: AbujaHausaNewsPREMIUM TIMESTakazza
Previous Post

Kotu ta bada belin matashin da ake zargin ya kutsa cikin coci yin sata kan naira 100,000

Next Post

Yadda jirgin kasan Abuja-Kaduna ya murkushe wata mota – Mahukunta

Premium Times Hausa

Premium Times Hausa

Next Post
Yadda jirgin kasan Abuja-Kaduna ya murkushe wata mota – Mahukunta

Yadda jirgin kasan Abuja-Kaduna ya murkushe wata mota - Mahukunta

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • JIGAWA A HANNUN BADARU: Yadda shekaru takwas na mulkin APC ya kasa rage katutun talauci da fatara
  • BANKWANA DA BUHARI: ‘Tinubu yau mafarkin ka ya zama gaskiya, Allah ya sa ka kai Najeriya fiye da inda na kai ta’ – Nasihar Buhari ga Asiwaju
  • Kotu ta tsige Kori Sufeto Janar din ‘yan sandan Najeriya Usman Baba, ta ce zaman sa IG ya haramta bisa doka
  • Diezani ta maka EFCC da Ministan Shari’a kotu, ta na neman diyyar naira biliyan 100, saboda sun kira ta ‘ɓarauniya’
  • Ba zan jira Litinin ba, tun Lahadi zan mika mulki ga Abba Gida-Gida in kama gaba na – Ganduje

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.