Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce za a ɗan ƙara adadi, amma ba za a fasa aiwatarwa da tsarin taƙaita adadin kuɗaɗe daga hannun jama’a ba.
Ya ce tsarin na taƙaita adadin kuɗaɗen da mutane za su riƙa cira a ATM, POS da bankuna ya nan, amma dai za a ɗan sassauta, ta yadda za a iya yin ƙari daga naira 20,000 a kullum, N100,000 a sati da kuma Naira 100,000 da Naira 500,000 a bankuna.
Emefiele ya yi wannan bayani a ranar Juma’a, bayan ganawar sa Shugaba Muhammadu Buhari a Daura, inda shugaban ke hutun ƙarshen shekara a garin su.
Ya yi wannan bayani bayan da Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Ƙasa su ka gayyace shi cewa ya bayyana a gaban su a ranar Alhamis.
Sannan kuma Majalisar Wakilai ɗin ta umarce shi ya dakatar da duk wani shirin taƙaita adadin kuɗaɗen naira da za a iya cirewa a kullum.
CBN dai ta ce sabon tsarin cirar kuɗaɗen zai fara aiki ne a ranar 9 Ga Janairu, 2023.
“Ina sane da gayyatar da Majalisar Tarayya ta yi min. Zan je, kuma zan yi masu bayani. Shi wannan tsari na taƙaita adadin kuɗaɗen da ke hannun jama’a, ai tun cikin 2012 aka fara shi.
“Amma kusan sau uku ko sau huɗu mu na so mu taƙaita kuɗaɗen da ke hannun jama’a, amma sai mu jingine tsarin, saboda mu na son ganin mun ƙara shiri sosai na sauƙaƙa hada-hada ta zamani a Najeriya.
“Shekaru 10 kenan tsakanin 2012 zuwa 2022. To a yanzu mun tabbatar cewa tsarin hada-hadar kuɗaɗe ta kafofin zamani ya samu karɓuwa, kuma ya wadata sosai a faɗin ƙasar nan.”
Ya ce ana ci gaba da samar da hanyoyin sauƙaƙa wa mutanen karkara bin tsarin hada-hadar kuɗaɗe ta zamani, musamman tu’ammali da POS, ta yadda tsarin bai kawo masu tawaya wajen hada-hada ko rayuwar su ɗungurugum ba.
“Yayin da na ke fitowa daga Daura yau ɗin nan, ai na ga wani shago mai ejan na POS.
“Akwai ejan na POS ɗin mu har miliyan 1.4 a faɗin ƙasar nan. Akwai su a ƙananan hukumomi da ƙauyuka da lungunan cikin karkara.”
Ya ce ejan na POS miliyan 1.4 kuwa ai tamkar ƙarin bankuna ne miliyan 1.4 a cikin ƙasa.
“Ba fa za mu zura idanu mu ƙyale fiye da kashi 85 cikin 100 na Naira su na watangaririya a wajen bankuna ba. Ƙasashe da dama a yanzu an daina hada-hadar jidar kuɗaɗe niƙi-niƙi, sai dai tsarin zamani ake bi.” Inji shi.
“Za mu sake nazarin adadin kuɗaɗen da za a riƙa cirewa. Amma ba za mu ƙara lokaci ko mu fasa tsarin ba,” inji Emefiele.
Discussion about this post