Hukumar SSS ta bai wa NNPC da dillalan fetur da sauran waɗanda lamarin ya shafa, kwanaki biyu su gaggauta kawo kawo ƙarshen wahala da ƙarancin fetur a faɗin ƙasar nan.
Kakakin SSS, Peter Afunanya ne ya fitar da wannan sanarwa a lokacin da yake bayani a taron manema labarai, ranar Alhamis, a Abuja.
Ya bayyana cewa SSS ta yi ganawar sirri da dukkan waɗanda ke da ruwa da tsaki a harkar fetur, kuma sun amince za su kawo kawo ƙarshen matsalar fetur ɗin a cikin kwanaki biyu.
“Mun yi taron sirri da NMDPRA, NUPEN, IPMAN, MOMAN da ma’aikatan daffo da sauran su,” inji Afunanya.
“Mun fito ƙarara mun shaida masu cewa lamarin fa ya isa haka nan. Mun shaida masu cewa su gaggauta su gaggauta magance matsalar nan ta hanyar da ta dace.
“Mun shaida masu cewa ‘yan Najeriya na da ‘yancin sayen mai a cikin ruwan sanyi. Mun ce masu ba za mu iya ci gaba da amincewa da wannan matsalar ƙarancin fetur ba.”
Ya ce dalilin shigar SSS cikin wannan lamari shi ne, saboda hukumar na da ikon gano duk wata ɓarakar da ka iya haifar wa tsaron cikin gida wata gagarimar matsala ko barazana ta tsaro.
“Kuma mu na da izni da damar bincike ko akwai wata maƙarƙashiyar yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon-ƙasa, wadda kuma matsala ce da ta shafi harkokin tsaro a cikin gida.
“Abin da mu ka gano a zaman da mu ka yi da su, akwai wadataccen fetur wanda zai wadaci ƙasar nan har zuwa lokacin da za a kammala bukukuwan Kirsimeti.
“NNPC ya ce akwai ganga biliyan 1.9 ajiye, kuma dukkan sauran waɗanda su ka halarci taron sun amince da cewa tabbas akwai wannan adadin a ajiye.
“An amince masu gidajen mai su riƙa aiki 24 a kullum. NNPC da masu tankokin ɗauko mai duk sun amince za su yi aikin su ka’in-da-na’in. Jami’an mu da sauran jami’an tsaro za su bayar da kariyar tsaro a cikin sa’o’i 24 a kullum,” inji Afunanya.