Hedikwatar Hukumar tsaron ƙasa DHQ ta bayyana cewa askarawan Najeriya sun kashe ƴan ta’adda sama da 60 a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya a cikin makonni uku a ƙasar nan.
Darektan yaɗa labarai na hukumar tsaron Najeriya manjo-janar Musa Danmadami ya sanar da haka a Abuja a cikin makon jiya.
Danmadami ya ce a tsakanin wannan lokaci dakarun Najeriya sun kama ƴan ta’adda tare da masu yi musu hidima sama da 50 sannan sun ceto mutum 27 da aka yi garkuwa da su.
Ya ce sojojin dake aiki a karkashin ‘Operation Hadarin Daji’ a yankin Arewa maso Yamma sun samu wannan nasara ne a dalilin tsawaita awowin da suke yin sintiri, kai wa mahara hari a matsugunan su dake dazukan dake iyaka da Katsina, Sokoto, Zamfara da Kaduna.
Danmadami ya ce a ranar uku ga Disamba dakarun sun kashe ƴan bindiga 7 inda sauran maharan suka gudu da rauni a kauyukan Ungawan Babale da Rafin Sarki dake karamar hukumar Giwa jihar Kaduna.
Ya ce dakaru sun kama wani mai siyar da bindigogi da rundunar ke neman sa ruwa a jallo a wani gidan man fetur dake karamar hukumar Jama’a.
Danmadami ya ce dakarun sun kama makamai da suka hada da AK-47 guda biyar, harsasan bindiga masu tsawon milimita 7.6 guda 4,000, barkonon tsohuwa da wukake.
Daga nan a cikin wadannan makonnin dakarun sun kama AK-47 guda 7, bindiga kirar baretta guda daya, babban bindiga kirar hannu guda daya, kanana 4.
Sun kuma kama babura 55, babura 7, wayoyin hannu 13, shanu 820 da kudi naira miliyan 2.3.
“Dakarun sun kashe ƴan bindiga 27, sun kama 36 sannan sun ceto mutum 35 da aka yi garkuwa da su.
Rundunar sojin sama dake aiki a karkashin ‘Operation Whirl Punch’ sun kai wa ‘yan bindiga hari a maɓoyan su dake karamar hukumar Giwa inda suka kashe su da yawan gaske.
Dakarun run rawaito cewa manyan hatsabibban ‘yan bindiga guda 7 na daga cikin maharan da sojojin suka kashe a harin.
Daga cikin manyan hatsabibin da aka kashe sun hada da Isah Kauri da Tambuwal dake Zamfara, da Noti, Bala, Yunusa da Burti.
A Arewa ta Tsakiya Danmadami ya ce dakarun sun samu nasaran kan wasu ƴan bindiga dake suka addabi mutanen yankin.
Ya ce dakarun sojin sama dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Safe Haven’a ranar 3 ga Disamba sun kai wa ‘yan bindiga hari a maboyar su dake dazukan Odare, Magama sannan da dajin Zurak dake kauyen Kampani a karamar hukumar Wase jihar Filato.
Rahoton da dakarun suka bada ya nuna cewa sun kashe mahara da dama inda wasu sun gudu da rauni a jikkunan su.
Discussion about this post