Majalisar Dattawa za ta yi zama na musamman a mako mai zuwa domin tattauna sabbin ƙa’idojin cirar kuɗaɗen da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce za a fara aiki da su daga ƙarshen watan Janairu.
Buƙatar zaman tattauna batun amincewa ko ƙin amincewa da sabon tsarin, ta taso ne bayan da ‘yan Najeriya da ma wasu sanatocin su ka fara ƙorafin cewa lamarin sabon tsarin zai kawo naƙasu da tawaya sosai a kasuwanci har ma da hada-hadar yau da kullum ga jama’a.
Sanata Philip Aduda mai wakiltar FCT Abuja ne ya bijiro da muradin neman a tattauna yiwuwar ƙin amincewa da tsarin, domin zai jefa miliyoyin jama’a cikin rayuwar ƙunci da kuma takura.
Mutane da dama dai su na cewa network na data ba shi da garanti a Najeriya, kuma miliyoyin mutanen karkara ba su mu’amala da bankuna, ATM, POS ko kuma waya ɗungurugum.
Da yawa na cewa naira 20,000 da aka ƙayyade za a riƙa cira kullum a ATM ko POS sun yi kaɗan.
Yayin da Sanata Aduda ya bijiro da buƙatar a tattauna batun a ranar Laraba, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya ce ba zai yiwu a yi gaggawar tattauna batun tun a ranar Laraba ba, kwana ɗaya bayan CBN ya yi sanarwar.
Ya ce a bari sai mako mai zuwa a tattauna batun. Kuma ya ce kafin a tattauna, “sai an gayyato Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele da Daraktoci biyu na CBN ɗin da Buhari ya ƙara wa wa’adi sun yi wa majalisa cikakken bayani dangane fa’idar tsarin tukunna.
Lawan ya ce daga nan majalisa za ta tattauna batun, ko dai a bari a fara aiwatar da shi, ko kuma a hana baki ɗaya.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Bankin CBN ya taƙaita cirar kuɗi da ATM zuwa N20,000 a kullum, N100,000 a sati.
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito da tsatsauran ƙa’idojin cirar kuɗi da karin ATM, wanda zai fara amfani tun daga ranar 9 Ga Janairu, 2023.
Cikin wata sanarwa da Daraktan Sa-ido na CBN, Haruna Mustafa ya sa wa hannu, ta umarci dukkan bankuna su tabbatar cewa kada mutum ɗaya ya cire sama da Naira 100,000 a rana, shi kuma kamfani ko ƙungiya kada su wuce cirar Naira 500,000 a rana a bankuna.
Za a fara bin wannan tsari a daidai lokacin da za a fara amfani da sabbin launin kuɗaɗe a ƙasar nan.
A cikin sanarwar, CBN ya ce daga ranar 9 Ga Janairun 2023, takardar kuɗi ta naira 200 ko ƙasa da haka ne kaɗai za a riƙa sakawa a asusun ATM ana cirewa.
Saboda haka kenan, duk wanda ya je cirar kuɗi da katin ATM, manyan kuɗaɗen da zai iya cira su ne takarar Naira 200.
“Duk wanda ya cire sama da Naira 100,000 a banki za a caje shi biyan kashi 5 bisa 100 na yawan kuɗaɗen da ya cira.
“Idan kuma kamfani ko wata ƙungiya ce ta cire kuɗaɗen fiye da Naira 500,000, za a caje ta biyan kashi 10 na adadin kuɗin da ta cira.
“Bankuna za su daina karɓar cakin kuɗin da ya wuce Naira 50,000. Kuma adadin kuɗin da mutum zai iya biya a cikin wani akawun ba zai wuce naira milyan 10 ba.”
“Kuɗin da mutum zai iya cirewa ta P.O.S a kullum ba zai wuce Naira 20,000 ba.”
Amma an bayar da damar mutum ya cire naira miliyan 5 shi kaɗai ko Naira miliyan 10 idan kamfani ne, amma sai da dalili gamsasshe, kuma sai da amincewa.
Sannan kuma sanarwar ta nemi bankuna su karɓi wasu sahihan bayanan mai cire kuɗi.
An umarci jama’a su maida hankali wajen amfani da hada-hadar kuɗaɗe ta waya, wato online, ta intanet, amfani da kati, POS, eNaira da sauran su.