Gwamnatin Najeriya ta fito ta bada haƙurin kashe fararen hula a ruwan bama-baman da jirgin sojojin sama ya yi wa fararen hula a garin Matumji da ke ƙarƙashin Masarautar Ɗansadau, cikin Jihar Zamfara.
Ministan Harkokin Yaɗa Labarai Lai Mohammed ne ya bada haƙurin a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, a ranar Laraba.
Ya ce Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwa da takaicin ganin fararen hula talakawa mazauna karkara su ka rasa rayukan su sakamakon ƙoƙarin da dakarun Najeriya ke yi don kakkaɓe ‘yan bindiga.
An dai kashe ‘yan bindigar da su ka ɓoye ne a cikin garin Matumji, inda lamarin ya rutsa da wasu mazauna garin masu yawan da wasu su ka ce sun kai 26.
PR Nigeria, wata jarida da ke da kusanci da hukumomin tsaron Najeriya ta ce tsakanin ‘yan bindiga da fararen hula an kashe sama da mutum 200.
Majiyar da ta tattauna da PREMIUM TIMES kuma ta tabbatar da cewa fiye da mutum 100 ne aka kashe.
Garin Mutumji ya na cikin Jihar Zamfara, amma ya yi iyaka da dajin Katsina, Kaduna, Neja da Kebbi, dajin da babu wata hukumar da ke kula da shi, sai ‘yan bindiga ne ke cin karen su ba babbaka a dajin.
A na ta ɓangaren, Gwamnatin Najeriya ta bakin Minista Lai Mohammed, ta ce lamarin abin takaici ne, kuma ta na bada haƙuri.
Yaƙi Da ‘Yan Sunƙuru Abu Ne Mai Wahala – Gwamnatin Najeriya:
Minista Lai Mohammed ya ce yaƙi da masu sunƙuru abu ne mai wahalar gaske. Sai dai a lura da cewa irin duk yadda Sojojin Sama ko dakarun sojojin ƙasa ke taka-tsantsan don gudun kada yaƙin ya ritsa da fararen hula, to akan samu ɓacin rana da tsautsayin da lamarin kan ritsa da fararen hula waɗanda babu ruwan su da rikicin. To muna bada haƙuri kuma mu na da-na-sanin afkuwar haka.”
Yadda Yaƙi Da ‘Yan Bindiga Ya Ci Rayukan Fararen Hula A Zamfara:
Fiye da mutum 100 ne tsakanin ‘yan bindiga da fararen hula bama-baman Sojojin Sama ya halaka bayan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 270
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren bama-bamai da Sojojin Saman Najeriya su ka kai yankin Malele Matumji a Massrautar Ɗansadau ya halaka fiye da mutum 100.
Jaridar PR Nigeria mai kusanci sosai ga hukumomin tsaron ƙasar nan, ta ruwaito cewa an tsakanin ‘yan bindiga da fararen hula, an kashe mutum 270.
Yayin da Rundunar Sojojin Najeriya ba su ƙaryata labarin ba, jaridar ta ci gaba da cewa maharan sun kashe Sojojin Najeriya 10.
PREMIUM TIMES a ranar Litinin dai ta bada rahoton kisan mutum 64.
Majiya ta shaida wa wakilin mu cewa waɗanda aka kashe a cikin fararen hula a ƙauyukan Matumji da Malele sun fi mutum 100.
“An kashe ‘yan bindiga a Malale za su mai 26. A Matumji kuwa an kashe ‘yan bindiga 68, waɗanda su ka yi ƙoƙarin tsere wa rugugin wutar bama-baman sojoji.
Wani da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce “yan bindiga sun mamaye Malele ne da niyyar kashe duk wani abu mai rai a ƙauyen. Sun yi niyyar ba za su bar kowa da rai ba. Saboda shekaru da dama sun yi ta ƙoƙarin mamaye ƙauyen, amma ba su samu nasara ba.
“Shi ne a wannan karo su ka wo gayyar dangin su daga ƙasashen waje cikin Afirka, da nufin su ragargaza ƙauyen baki ɗaya.” Haka Nuhu Ɗansadau ya shaida wa wakilin mu.
Kakakin Sojojin Sama ya shaida wa wakilin mu cewa nan ba da daɗewa ba zai fitar da sanarwa ga manema labarai dangane da ƙarin hasken da zai yi. Amma bai bayyana adadin sojojin da aka kashe, yawan ‘yan ta’adda ko adadin farashin hular da wannan ƙazamin yaƙi ya ritsa da su ba.
Gwamnatin Jihar dai ta fitar sanarwar ta’aziyya da jajentawa ga iyalan fararen hular da yaƙin ya ritsa da rayuwar su.
Bayanan farko kafin wannan ƙarin haske dai sun nuna cewa bama-baman Sojojin Sama ya halaka ‘yan bindiga da fararen hula 64, a yankin da gogarma Lawali Damina ya yi garkuwa da mutum 270.
Da farko labarin ya nuna cewa harin da Sojojin Saman Najeriya su ka kai wa ‘yan ta’adda a ƙauyen Mutumji ya yi sanadiyyar kashe ‘yan bindiga da dama, tare da fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba.
Harin bama-baman ya faru ne kwana ɗaya bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda gogarma Lawali Damina ya yi garkuwa da ilahirin mazan cikin ƙauyen Randa, ƙauyen da ke ƙarƙashin mazaɓar Mutumji.
Sojoji sun kai harin ne bayan mazauna yankin sun yi masu kiran gaggawar shaida masu cewa ‘yan bindiga sun darkaki ƙauyukan Malele, Ruwan Tofa da ‘Yan Awaki.
Majiya ta ce sojojin sama ɗin sun daƙile kai farmakin, inda mahara su ka tsere cikin garin Mutumji.
Sojojin Sama sun bi su da ruwan bama-bamai, inda lamarin ya ritsa har da fararen hula da dama.
Wani jami’i kuma mamba na Hukumar Kare Haƙƙin Jama’a, Nuhu Ɗansadau, ya shaida wa Premium Times cewa an kashe ‘yan ta’adda da fararen hula kamar 64. Sannan kuma waɗansu mutum 12 sun ji raunuka.
Ya ce a ranar Litinin an garzaya da waɗanda su ka ji raunukan zuwa Gusau domin ci gaba da kulawa da su.
Wani basarake a Mutumji mai suna Abdulƙadir Abdullahi, ya ce, “Gaskiya lamarin ya yi muni ƙwarai, domin har yanzu ana ci gaba da nemo gawarwakin wasu da ake nema ba a gani ba.
Fashi, Garkuwa Da Kashe-kashe A Ƙaramar Hukumar Maru:
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ɗan bindiga ya kwashe mazan gari guda, fiye da mutum 270 saboda faɗa kan budurwa, 20 sun mutu saboda ƙududun takaici da bugun zuciya.
Tantagaryar ɗan iskan ɗan ta’adda mai suna Lawali Damina, ya yi garkuwa da ilahirin mazajen ƙauyen Randa arankatakaf, har da yara ƙanana, saboda ɓatan bindigogin sa biyu bayan an yi rikici kan wata budurwa.
Ƙauyen Randa wanda ke cikin Mazaɓar Matumji a Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar Zamfara, ya na ƙarƙashin Masarautar Ɗansadau.
Mazauna yankin da kuma wani basarake da ke Matumji, sun shaida wa wakilin mu cewa asalin rikicin dai wani ɗan bindiga ne ke soyayya da wata baƙuwa mai suna Zaliha, wadda ta je ƙauyen daga wani gari wajen Shinkafi.
“To ranar da abin ya faru, ɗan bindigar ya shigo Randa, sai ya samu wasu ‘yan bindiga su biyu tsaye tare da Zaliha. Bayan sun yi sa-in-sa a tsakanin su, sai saurayin yarinyar mai suna Gora ya fusata, ya koma cikin daji. Ashe ya yi kwanton-ɓauna a hanya, sai da waɗancan ‘yan bindigar su ka zo wucewa, sai ya bindige su biyun kuma ya tsere. Dama kuma ba cikin rundunar waɗanda ya kashe ɗin ya ke ba.