Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin cewa daga ranar da aka rantsar da shi idan ya ci zaɓen 2023, to daga ranar za a daina kashe ‘yan Najeriya saboda sumogal ɗin buhun shinkafa.
Atiku ya sake yin alƙawarin cewa kuma daga ranar za a buɗe kan iyakokin Najeriya.
Rufe kan iyakokin Najeriya da aka yi tun kafin annobar korona har zuwa yau, ya haifar da tsananin ƙuncin rayuwa, musamman a jihar Katsina, inda jami’an kwastan su ka yi ƙaurin suna wajen bindige masu fasa-ƙwaurin buhunan shinkafar da su ke shigowa da shi ta kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Wani alƙawari da Atiku ya ƙara yi a gaban dandazon magoya bayan PDP, a filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina, shi ne alkawarin magance matsalar tsaro da kuma farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
Jihar Katsina na sahun gaba a jerin jihohin da ‘yan bindiga ke ci gaba da ragargazar su babu ƙaƙƙautawa, tsawon shekaru da dama.
Ko kwanaki biyu kafin zuwan Atiku kamfen a Katsina, wakilin PREMIUM TIMES na Katsina ya tsallake kwanton-ɓaunan ‘yan bindiga da kyar a dajin jihar Katsina, yayin komawa Katsina daga Zamfara.
A kamfen ɗin da Atiku ya je Katsina, ya ce PDP ta bunƙasa jihar Katsina sosai, don haka jama’a su sake fitowa su zaɓi jam’iyyyar domin ta sake share masu hawaye kamar yadda ta yi a baya.
A ziyarar da ya kai Fadar Sarkin Katsina Abdulmumin Kabir, Atiku ya bayar da gudummawar tallafin kuɗi naira miliyan 50 domin raba wa ‘yan gudun hijirar da ke sansanoni daban-daban a faɗin jihar. Masu gudun hijirar dai ‘yan bindiga su ka fatattake su daga garuruwan su.
Baya ga masifar ‘yan bindiga a Jihar Katsina, jihar na daga sahun jihohin da talauci da ƙuncin fatara ya yi wa talakawan ta katutu, kamar yadda rahoton Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Fatara da Talauci da sauran bayanai, wato ‘National Bureau of Statistics ta bayyana.
Wazirin Adamawa dai ya ziyarci Sarkin Daura, kuma ya ziyarci Dada ‘Yar’Adua, mahaifiyar tsohon Shugaban Ƙasa, Umaru Musa Yar’adua. A lokacin ziyarar ta ɗin ce har da Turai, uwargidan Umaru ‘Yar’Adua ta na wurin.
Discussion about this post