Duk da cewar First Lady Aisha Buhari ta fuskanci kalubalen da ke cikin matsayin da ta dauka a baya, na neman hakkin ta, bisa zargin cin mutuncin da Dalibi Aminu (aka Catalyst) na Jami’ar FUD yayi mata a Dandalin Twitter, wanda a yanzu ta ce ta janye kuma ta yafe masa, amma fa duk da haka wannan hatsaniya ta bar baya da kura. Ko yanzu talakawan Arewa zasu sake fahimtar matsayin su a wajen Baba Buhari? Wanda a baya suke ganin sa tamkar wani waliyi mai ceton su.
Duk da cewa a yanzu ta fahimci gaskiyar yin afuwa da juriya har ta janye kudirin ta, ko kadan wannan hukuncin da First Lady ta dauka a baya, kan shaguben da wannan Dalibi yayi mata, babu wani abin mamaki.
Kuma a matsayinta ta mutum da ke son kare mutuncin ta, tana da uzuri tabi kadun hakkin ta a gaban kuliya, saboda haka babu wani abin mamaki a ciki. Amma in har ta tabbata a turbarta ta neman hakin ta lakada masa duka, in har haka abin yake, to ba tayi dattako ba, a matsayin na uwa. Bayan haka babban abin takaicin shine yin gum din Shugaba Buhari a kan lamarin a baya, har sai da wannan batu ke neman tono garma, sai nan a ka ce ya magantu. Wanna fa, ya isa ya nunawa Talakan Arewacin Nijeriya matsayin sa a gida Baba Buharin da bashi da gata a baya kamar na talakan.
Wai shin da talakan Arewacin Nijeriya suna tunanin Shugaba Buhari na kaunar su kamar yadda suke yi masa? Talakawa ne gatan sa, su suka tsaya masa, har wasu suka rasa rayukan su, su suka bashi kudin da ya kaishi Villa, har ma Aisha ta zama First Lady. Inda da irin wannan kauna da bai bar wannan matsala ta kai haka ba. Kai, in da a ce talakan arewa na da matsayi a gidan Buhari da haka bata faru ba.
In har muka yi tunani a baya da ma a yau, da Buhari na kaunar talakan Arewa da bai yi sake a mulkin sa Takin Zamani ya ya kai N20,000 da ga N3,000, amma kullum gori yake musu suna sharholiya basu noma.
Inda akwai kauna, bazai yadda arewa maso gabas ta daidaice ba, matasan su sun dunguma jeji, sun zama yan ta’adda, sun hana noman ma a yi.
Inda da wannan kauna bazai hana dan talaka karatu ba, irin na jami’a, amma wannan batu na gaba kowa zai sheda, domin kamar yadda yayi ikirari, dan talaka irin na arewa bai isa karatu a jami’a ba, misali a tambaya nawa ne dalibi zai biya a sabuwar jami’ar tarayya da ya kirkiro a garin Azaren Jahar Bauchi. To wannan shine shirin Buhari ga dukkanin makarantun gaba da sakandare, wannan duk sakayya ce ga talakan Arewa daga Buhari. A nan gaba sai duk dalibin da ke son karatu a Jami’a ya biya kimanin N200,000 koma fiye a kowace shekara, wannan kiyasine sakamakon rigimar gwamnati da ASUU, kuma shine matsayar Gwamnatin Buhari.
In muka muka tuna baya, siyasar kauna da mutanen Nijeriya, musamman ma na Arewa, kuma matasa suka nunawa Buhari a baya, babu irin cin zarafi, da shagube a kafafen sadarwar zamani da mawakan zamani basu yiwa shugabannin wancan zamanin ba, don kawai a tallata Buhari. Amma su sun nunawa ‘Yan Nijeriya Juriya, kawaici da sanin ya kamata, babu wani shugaba ko matar sa da nuna irin wannan fushin. Amma yau gashi halin da muke ciki da gidan Shugaba Buhari, wanda karara suka nuna rashin juriya da hakuri a kan kalaman da basu kai sun kawo ba, kuma Magana mai harshen damo, wanda bai zama lalle abin da Aminu yake nufi yayi dai dai da fassarar ka/ke/ko ni ba.
In mun dawo kan takaddamar nan. A Siyasan ce, ita fa siyasa duk wanda ya shige ta, to ya zama dole yayi hakuri da abubuwa masu yawa, wannan ya hada kananan maganganu da ma manyan maganganu, dole sai kaji, kayi kamar baka ji ba, wani lokacin in angayama mai daci, sai ka cije, kama yi dariyar getsetse.
Irin wannan maganganu an gaya wa shugabannin baya, amma yi musu zancen da wuce haka da su da iyalen su, kai har ma a irin kasashen da suka ci gaba a siyasa irin su USA a na yi wa shugabannin irin wannan maganganu. Aisha Buhari yar siyasa ce, domin da ita aka yi neman zaben mijinta, har ta jogoranci wasu tarurrukan a baya, ya kamata irin wannan maganganu su zama darasi ga gidan kowace siyasa.
A yau fa Aisha Buhari, ita ce First Lady, har an nada mata masu hidima da taimakamata wajen aikace aikacen ta, kuma duk ana biyan su da kudin talakawan Nijeriya. Koda a fagen siyasa, wadda ita wannan siyasa ta maida Aisha Buhari First Lady, harma take jagorantar wasu matan shugabannin kasashen Africa, siyasa ce ta bata damar shiga Villa, har ma tasa a jawo aka yi mata tsabiri irin na siyasa a Dandalin Twitter. A tarihin siyasar wannan kasa fa, babu shugaban kasar da ya more mulki, wajen aurar da yayan sa, da kasetacchen buki na kece reni kamar Buhari da matar a Aisha Buhari. Dole yayin da ake shan zaki, wani lokacin a dandani dachi, haka mulki ya gada.
A Addinance ma, kowa ya san muhimmancin yin hakuri, yafiya, afuwa da maida alkhairi ga sharri, kullum irin wannan kalamai malamai ke yiwa al’ummah, musamman talakawa, amma abin mamaki, a magangannun malamai a yau, saboda abin ya shafi masu mulki, amfi karfafa rashin tarbiyar wannan yaron akan aja hankalin shugaba ya zama abin musali wajen yin afuwa da yafiya, kamar yadda Malamai suka nuna annabi yafi kowa hakuri da afuwa, wannan afuwa da tayi, tamkar tayi koyi da Manzon Tsira ne.
Ita kanta First lady inda ta nuna dantako da kuma zama uwa ta gari kamar irin su Nana Aisha (RA) matar Manzon Allah (SAW) da ta jawa Aminu Kunne da yi masa nasiha da kuma ilmantar da shi a kan kwawawan kalamai, da har abada ta zama abar musali a cikin al’umar wannan lokaci, da ma wanna surutan basu faru ba. Aminu (Catalyst) ba yaron banza bane, yaron da yake Ajin karshe a Jami’a, ya kamata a yi masa uzuri, domin babu wanda ya fi karfin kuskure. Amma duk da haka ba a makara ba, duk da cewa daga baya tayi afuwar.
In na dawo kan batu na, cewa dama talakan Arewa ne ke yaudarar kan sa a kan san Buhari, shi daman ba talaka a gaban sa, kuma kauda kai ya keyi, harma yayi dariya a wasu lokutan in talaka ya shiga matsi, wannan batu na Aminu kawai daya ne, ganin cewa an makara, duk da cewa zuwa da wuri yafi da wurwuri.
Shin Buhari na kaunar talakan Arewa ne, yayin da yayan talakawa musamman ma na Katsina, Zamfara, Kaduna su ka koma daji suka zama yan ta’adda, wanda a baya sune na gaba-gaban sai Buhari.
Allah ya kiyaye gaba.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post